Gwamna Wike: Da Zarar 'Yan Ta'adda Sun Ji Sunana Za Su Tsere

Gwamna Wike: Da Zarar 'Yan Ta'adda Sun Ji Sunana Za Su Tsere

  • Dan takarar shugaban kasa na zaben 2023 kuma gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya lashi takobin yaki da ‘yan bindiga idan ya ci zabe
  • Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya samu ganawa da wakilan jam’iyyar PDP a Jihar Taraba ranar Alhamis
  • Wike ya ce matsawar gwamnatin tarayya ta na son kawo karshen ta’addanci da yaduwarsa, sai ta samar da ‘yan sandan jiha

Jihar Taraba - Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya yi alkawarin yaki da ta’addanci idan har ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2023, Daily Trust ta ruwaito.

A ranar Alhamis, gwamnan ya shaida hakan yayin wani taro da wakilan PDP na Jihar Taraba.

Wike ya kawo mafita akan mahawarar da ake yi na bukatar samar da ‘yan sandan jiha, inda ya koka akan yaduwar ta’addanci.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Gwamnati za ta iya maka ASUU a kotu idan aka gagara yin sulhu inji Minista

Shugabancin Kasa Na 2023: Da Zarar 'Yan Ta'adda Sun Ji Sunana Za Su Tsere, In Ji Wike
2023: Da Zarar 'Yan Ta'adda Sun Ji Sunana Za Su Tsere, Wike. Hoto: PM News.
Asali: Twitter

In har ana son kawo karshen ta’addanci, wajibi ne samar da ‘yan sandan jiha

PM News ta bayyana yadda ya ce:

“Gwamnatin Tarayya ba za ta iya kawo karshen ta’addanci ba in har ba ta samar da ‘yan sandan jiha ba. Dole sai an samar da su, babu wata dabarar da ta zarce hakan.”

Ya ci gaba da cewa samar da ‘yan sandan jiha ba yana nufin ba za a samar da na tarayya bane. Ko kananun hukumomi idan su na so za su samar da nasu. Hakan zai taimaka wurin samar wa mutane aiki.

Ya ce idan aka tafka laifi ga gwamnatin tarayya, sai ‘yan sandan tarayya su yi aiki akai. Idan kuma aka yi laifi karkashin jiha, sai ‘yan sandan jiha su yi aiki akai. A cewarsa, in har ana son kawo karshen ta’addanci a Najeriya sai an samar da ‘yan sandan jiha.

Kara karanta wannan

Zulum: Muna Sane Da Hatsarin Da Ke Tattare Da Shirin 'Sauya Tunanin Tubabbun Ƴan Ta'adda'

Wike ya ce yana da damar kawo karshen duk matsalolin Najeriya

Ya ci gaba da cewa:

“Babbar matsalar da gwamnatin PDP za ta kawo wa mafita (in har aka zabe ni) shi ne kawo karshen rashin tsaro don bunkasa tattalin arziki.
“Idan ‘yan bindiga suka ji suna na, guduwa za su dinga yi saboda yaki zan kaddamar saboda su. Ni ne zan dinga bayar da umarni akan yadda za a ragargaje su.
“Zan dinga kaddamar da shirye-shirye akan tsaro, noma da kuma tattalin arziki duk gabadaya. Zan tabbatar na kaddamar da duk wata hanyar ci gaba don ‘yan Najeriya su ji dadi saboda ina da damar kawo karshen matsalolin Najeriya.”

Harin Jirgin Ƙasa: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai

A bangarensa, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya lashi takobin yin hayar sojoji daga kasashen ketare don su taya yaki da ‘yan ta’adda bayan harin da suka kai wa jirgin kasa a Kaduna ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

Ya kuma lissafo jihohi 4 na yankin arewa maso yamma, inda ya ce akwai yuwuwar su bi sahun shi. Jihohin sun hada da Zamfara, Kebbi, Katsina da Sokoto, The Punch ta ruwaito.

Ya ce za su dauki wannan matakin ne matsawar gwamnatin tarayya bata dauki wani matakin a zo a gani ba a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164