Hukumar Yaƙi Da Rashawa Ta Jihar Kano Ta Yi Barazanar Kama Dambazau

Hukumar Yaƙi Da Rashawa Ta Jihar Kano Ta Yi Barazanar Kama Dambazau

  • Hukumar Korafin Jama’a da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, A ranar Alhamis ta yi barazanar kama manajan darektan Hukumar Kare Hakkin Kwastomomi ta jihar, KCPC, Idris Bello Dambazau
  • Shugaban PCACC, Mahmoud Balarabe ne ya yi barazanar a Kano inda ya ce Dambazau ya ki amsa gayyatar da suka mishi don sauraron korafin da aka yi akansa na rashawa
  • A cewar Balarabe, hukumar ta su ta samu korafi da dama akan shugaban KCPC wadanda duk zarginsa ake yi da rashawa da sauran laifuka, hakan ya sa suka gayyace shi amma ya ki zuwa

Kano - A ranar Alhamis, Hukumar Korafin Jama’a da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta yi barazanar kama shugaban Hukumar Kare Hakkin Kwastomomi ta Kano, KCPC, Idris Bello Dambazau, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Gwamnati za ta iya maka ASUU a kotu idan aka gagara yin sulhu inji Minista

Hukumar Yaki da Rashawar Jihar Kano Na Barazanar Kama Dambazau
Hukumar Yaki da Rashawa Ta Jihar Kano Ta Yi Barazanar Kama Dambazau. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Hakan ya biyo bayan yadda Dambazau, wanda soja ne mai murabus, ya ki amsa gayyatar da hukumar ta yi masa na zarginsa da aikata wasu laifuka tare da rashawa kamar yadda shugaban PCACC, Mahmoud Balarabe ya shaida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Balarabe ya ci gaba da cewa, akwai korafi da dama na zargin rashawa da wasu laifuka da aka tura musu akan shugaban KCPC din.

Ya ci gaba da cewa:

“Doka ta tilasta mana gayyatar duk wanda aka turo mana korafi na zargi akansa. Saboda a yi masa adalcin ji daga bakinsa.”

Balarabe ya ce ko dai Dambazau ya kai kansa ko kuma su kama shi a duk inda suka gan shi

The Herald ta kula da inda Balarabe ya ce dokar PCACC ta bayar da damar kama duk wanda hukumar ta gayyata amma ya ki zuwa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

A cewarsa:

“‘Yan sandanmu sun je har ofishinsa don su kama shi, amma aka shaida musu cewa bai je ba. Sun duba ko ina, ba su gan shi ba. Don haka ko dai ya kawo kansa ko kuma a duk inda aka gansa za a kama shi.
“Don an gayyaci mutum ba ya nufin an tabbatar da zargin da ake yi masa. Aikinmu ne kawo mafita dangane da rashawar da ta addabi yankinmu."

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani rahoton, Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Mohammed Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel