Ku ceto duk yan Najeriyan dake hannun yan ta'adda, Buhari ga Hafsoshin tsaro

Ku ceto duk yan Najeriyan dake hannun yan ta'adda, Buhari ga Hafsoshin tsaro

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nuna damuwarsa kan karuwar matsalar tsaro a faɗin kasa yayin taronsa da Hafsoshin tsaro
  • Cikin gaggawa kuma ba tare da bata lokaci ba, Buhari ya umarci su ceto dukkan mutanen da yan ta'adda ke tsare da su
  • NSA Babagana Monguno ya ce ya ba da wasu shawarwari a taron kuma shugaba Buhari zai yi nazari a kan su

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci hafsoshin tsaro su gaggauta ceto baki ɗaya mutanen dake hannun yan ta'adda a sassan ƙasar nan.

Buhari ya ba da wannan umarnin ne yayin da yake jawabi a wurin taronsa da shugabannin tsaro a Abuja ranar Alhamis, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaban kasa ya fadawa Malamai da Sarakuna da suka yi buda-baki a Aso Villa

Taron majalisar tsaro.
Ku ceto duk yan Najeriyan dake hannun yan ta'adda, Buhari ga Hafsoshin tsaro Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Mai baiwa shugaban shawara kan harkokin da suka shafi tsaro (NSA), Babagana Monguno, shi ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai na gidan gwamnati jim kaɗan bayan kammala taron.

Monguno ya ce:

"Shugaban ƙasa ya nuna takaici kan kalubalen da ya shafi tsaron ƙasar nan da kuma cigaban da aka samu, a takaice lamarin ya lakume rayukan yan ƙasa da dama, wasu kuma an yi garkuwa da su."
"Ba wai Fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja ƙaɗai ba, har da sauran mutanen da yan ta'adda suka sace a sassan ƙasar nan."
"Shugaban ƙasa ya umarci baki ɗaya dakarun tsaro da na fasaha su ceto mutane cikin gaggawa kuma ba tare da cutarwa ba. Wannan ne batun da aka tattauna da sauran su."

NSA ya ƙara da cewa babban hafsan tsaro, shugabannin hukumomin soji, Sufetan Yan sanda na ƙasa, duk sun gabatar da bayani ga shugaban ƙasa kan inda aka kwana a hukumomin da suke jagoranta.

Kara karanta wannan

Ina da kwarin guiwa da izinin Allah wannan ɗan takarar ne zai gaji Buhari a 2023, Sanatan Kano ya magantu

Na ba da shawarwarin yadda za'a magance matsalar tsaro - NSA

Monguno ya ce a ranar Alhamis ya ba da shawarwari kan hanyoyin da za'a bi a dawo da zaman lafiya a Najeriya, kuma shugaba Buhari na nazari kan shawarin.

"Na miƙa kunshin shawarwari ga majalisar kuma shugaban ƙasa ya yi duba zuwa gare su. Shawarin sun taɓo kowane sashe na tsaro, tun daga bakin boda zuwa cikin ƙasa."

A wani labarin kuma Gwamnatin Neja ta tabbatar Jirgin yaƙin Sojoji ya kashe kananan yara bisa kuskure

Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da kashe kananan yara shida a wani samame da jirgin yaƙin sojoji ya nufi yan ta'adda a jahar.

Sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Matane, ya ce tabbas lamarin ya faru kuma yanzu haka suna cigaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel