Nyame Da Dariye: Ka Janye Afuwar Ko Mu Jefa Maka Ƙuri'ar Rashin Gamsuwa, Ƙungiyoyin Arewa 19 Ga Buhari

Nyame Da Dariye: Ka Janye Afuwar Ko Mu Jefa Maka Ƙuri'ar Rashin Gamsuwa, Ƙungiyoyin Arewa 19 Ga Buhari

  • Hadakar kungiyoyi masu zaman kansu 19 a Arewa sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya janye afuwar da ya yi wa Dariye da Nyame da wasu masu laifi
  • Kungiyoyin sun sha alwashin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kuri'ar rashin amana muddin ba a janye afuwar ba
  • Sanarwa da hadakar kungiyan ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta da sakatare ya ce afuwar zai karya gwiwar hukumomin yaki da rashawa

Hadakar kungiyoyi masu zaman kansu na Arewa, 'Conference of Northern States Civil Society Networks' ta yi barazanar yin kuri'ar rashin gamsuwa kan gwamnatin Shugaba Buhari idan bai janye afuwar da ya yi wa wasu mutane da ake yanke wa hukunci ba ciki har da tsaffin gwamnonin Taraba da Plateau, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ku kwantar da hankulanku, yafewa Dariye da Nyame ba matsala bane - Buhari

Idan za a iya tunawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari bisa shawarar Majalisar Kolin Kasa ta yi afuwa ga masu laifi 159 ciki har da tsaffin gwamnoni Joshua Dariye da Jolly Nyame.

Nyame Da Dariye: Ka Janye Afuwar Ko Mu Jefa Maka Ƙuri'ar Rashin Gamsuwa, Ƙungiyoyin Arewa 19 Ga Buhari
Kungiyoyin Arewa 19 Sun Bukaci Buhari Ya Janye Afuwar Da Ya Yi Wa Nyame Da Dariye. Hoto: Fadar Shugaban Kasa.
Asali: Twitter

An daure tsaffin gwamnonin ne saboda satar biliyoyin naira na kudin al'umma sannan kotun koli na kasa ta jaddada hukuncinsu.

Ambasada Ibrahim Wayya Shugaban Hadakar da Ibrahim Yusuf, Sakatare ne suka rattaba wa sanarwar hannu a madadin kungiyoyin 19, inda suka yi tir da afuwar da aka yi wa tsaffin gwamnonin biyu, Solacebase ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce rashin kyautatawa ne ga hukumomin yaki da rashawa kuma hakan zai karya musu kwarin gwiwa.

"Mu mambobin wannan hadakar, a matsayin mu na jakadun yaki da rashawa mun yi allawadai baki daya kuma muna kira ga Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari GCFR, ya yi gaggawar janye afuwar da aka yi wa wasu da aka yanke wa hukunci saboda rashawa.

Kara karanta wannan

An gano abu 1 da ya hana a fito da Dariye, Nyame daga gidan yari tun da an yafe masu

"Idan Shugaban Kasar bai aikata hakan ba, Wannan kungiyar bata da wani zabi illa ta nemi hadin kai da sauran kungiyoyin al'umma masu zaman kansu a kasar da waje su kada kuri'ar rashin gamsuwa ga Gwamnatin Tarayya," in ji sanarwar.

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani rahoton, Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel