Ku kwantar da hankulanku, yafewa Dariye da Nyame ba matsala bane - Buhari

Ku kwantar da hankulanku, yafewa Dariye da Nyame ba matsala bane - Buhari

  • Mai magana da yawin shugaban kasa ya ce yan Najeriya su sani Shugaba Buhari ya bi ka'ida wajen sakin Dariye da Nyame
  • Shugaba Buhari ya bada tabbacin cewa ba don siyasa aka yi kuma ba kasa a gwiwa yayi wajen yaki da rashawa ba
  • Garba Shehu yace sashe na 175 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta bashi daman yin haka

Abuja - Fadar Shugaban kasa a ranar Laraba ta ce yafewa tsaffin gwamnoni biyu da Shugaba Muhammadu Buhari yayi ba zai zama matsala ga yaki da cin hanci da rashawa ba.

A makon da ya gabata, majalisar koli ta kasa karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta yafewa tsaffin gwamnoni biyu; Joshua Dariye da Jolly Nyame, da wasu mutum 157.

An jefa Joshua Dariya kurkuku ne bisa almundahanar kudin al'ummar jihar N1.16 billion lokacin yana gwamna a Plateau.

Kara karanta wannan

Nyame Da Dariye: Ka Janye Afuwar Ko Mu Kaɗa Maka Ƙuri'ar Rashin Gamsuwa, Ƙungiyoyin Arewa 19 Sun Gargaɗi Buhari

Shi kuwa Jolly Nyame ya sace N1.6 billion daga asusun jihar Taraba lokacin yana gwamna tsakanin 1999 da 2007.

Buhari
Ku kwantar da hankulanku, yafewa Dariye da Nyame ba matsala bane - Buhari Hoto: Channels
Asali: UGC

Amma a jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, yace Buhari ya bi ka'ida wajen yafe musu kuma shawara kwamitin afuwa watau Presidential Advisory Committee on the Prerogative of Mercy (PACPM) ta bashi.

Shehu yace sashe na 175 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta bashi daman yin haka.

Yace:

"Duk da cewa yafewa tsaffin gwamnonin nan biyu cikin saura zai tada kura, musamman yayinda zabe ke gabatowa, Shugaban kasa na ganin zalunci ne ware sunayensu duk da an bashi shawarar yafe musu kawai saboda tsaffin gwamnoni ne."
"Shugaba Buhari na bada tabbacin cewa ba don siyasa aka yi kuma ba kasa a gwiwa yayi wajen yaki da rashawa ba."

Kara karanta wannan

Mai fada a ji ga Buhari: Ka san yadda zaka yi Jonathan ya gaje ka a zaben 2023

Kawai ka bude gidajen yari kowa ya fito: Babban Lauya ga Buhari kan yafewa Nyame da Dariye

Shararren Lauya, Femi Falana, a ranar Juma'a, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya bude gidajen yari gaba daya a saki dukkan wadana aka daure kan laifin sata.

Falana ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron tunawa da marigayi Yinka Odumakin a jihar Legas, rahoton Vanguard.

Ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi adalci da daidaito tsakanin yan kasa saboda haka wajibi ne a saki dukkan wadanda tsare a kurkuku kan laifin sata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel