Luguden wuta: Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga, sun tura da yawa lahira a jihar Benuwai

Luguden wuta: Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga, sun tura da yawa lahira a jihar Benuwai

  • A wani sintiri da suka gudanar, Sojojin OPWS sun kashe yan bindiga uku har lahira a jihar Benuwai
  • Wata majiya ta bayyana cewa Sojojin sun yi artabu da yan ta'adda, wanda bisa tilas suka tsere da raunukan harbi
  • Haka nan kuma Sojojin sun kwato makamai da suka haɗa da bindigu da sauran kayan aikin yan ta'addan

Benue - Dakarun rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS) a jihar Benuwai sun yi nasarar sheƙe yan bindiga uku a ƙauyen Chito, kusa da Zaki Biam, hedkwatar ƙaramar hukumar Ukum a jihar.

Wani shaida ya gaya wa Daily Trust cewa yan bindigan suna ƙarƙashin wani da ake kira 'Full Fire' na biyu dake jagorantar sansanin marigayi Terwase Akwaza (Gana).

Dakarun sojin Najeriya.
Luguden wuta: Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga, sun tura da yawa lahira a jihar Benuwai Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

A cewarsa tawagar yan bindigan ta hana mutane sakat a yankin Sankera, wanda ya haɗa kananan hukumomin Ukum, Logo da kuma Kastina-Ala.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Dakarun sojin Najeriya sun bindige fitaccen kwamandan IPOB

Ya ƙara da cewa dakarun OPWS a yan kwanankin nan sun gudanar da wani sintiri, wanda garin haka ne suka ci karo da yan bindiga, sun yi kokarin tserewa amma abun ya ci tura.

Yadda Sojojin suka samu nasara

Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta daga rundunar sojin ta ce:

"Sojojin sun tsaftace da bincike yankin kuma sun gano wasu abubuwa da suka haɗa da bindigu, Mashina biyu da wayoyin hannu uku."
"Sojojin na zaune ne a Gbise dake Katsina-Ala, kuma suka gudanar da wani Sintirin yaƙi a yankunan Atunbe, Madamu, Kaamen, Ude -Jor, Kasar, Tor-Tacha da Tafkin Yoyo dake Utange duk a karamar hukumar Kastina-Ala."
"Yayin haka ne suka ci karo da wasu makiyaya a Tor-Cha, aka yi ɗauki ba daɗi bisa tilas makiyayan suka ranta a na kare ɗauke da raunukan harbi. Bayan haka mun yi bincike mun gano makamai."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Kakakin rundunar OPWS, Flying Officer Audu Katty, bai ɗaga kiran da ake masa ba domin tabbatar da nasarar sojojin.

A wani labarin na daban kuma INEC ta bayyana yadda zata yi da yawan mutanen dake neman takarar shugaban ƙasa a 2023

Hukumar zaɓe INEC ta ce ko kaɗan ba ta damu da yawan yan takarar dake neman shugaban ƙasa ba a zaɓen 2023.

A cewar hukumar mai zaman kanta, jam'iyyun siyasa 18 ne halastattu, dan haka su ne kaɗai zasu gabatar mata da yan takarar su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel