Jirgin Super Tucano ya yi wa ISIS lahani, ya kashe ‘Dan ta’addan da ake takama da shi

Jirgin Super Tucano ya yi wa ISIS lahani, ya kashe ‘Dan ta’addan da ake takama da shi

  • Sojojin saman Najeriya da na hadin-gwiwa na MNJTF sun aika Ammar Bin Umar zuwa barzahu
  • Bin Umar yana cikin dakarun kungiyar ISIS da aka aiko domin ya sasanta Boko Haram da ISWAP
  • An yi amfani da jiragen yaki ne bayan Sojoji sun samu labarin inda ‘Yan ta’addan suka fake a Marte

Borno - Dakarun sojojin hadin-gwiwa na MNJTF sun yi nasarar kashe wani babban mayakin kungiyar ‘yan ta’addan ISIS na Islamic State of Iraq and Syria.

Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Talata, 19 ga watan Afrilu 2022 da ya nuna cewa sojojin saman sun kashe Ammar Bin-Umar wanda jagora ne na sojojin ISIS.

An kashe Bin Umar ne a yankin tafkin Chadi a sanadiyyar luguden wuta da jirgin sama ya yi.

Ana tunanin cewa kungiyar ISIS ce ta turo Ammar Bin Umar domin ya hada kan mayakan kungiyar ISWAP da kuma bangaren Boko Haram da ke rikici.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga, sun tura da yawa lahira a jihar Arewa

‘Yan ta’addan sun fake ne a Tumbun da ke yankin tafkin Chadi inda suke kai wa jama’a da jami’an tsaro hari a kasashen Najeriya, Nijar, Chad da kasar Kamaru.

An hallaka Bin Umar

Wani soja ya tabbatarwa jaridar cewa an ga bayan ‘dan ta’addan ne a wani hari da sojojin saman Najeriya da MNJTF suka kai cikin jiragen yakin Super Tucano.

Jirgin yaki
Wani jirgin yaki (ba Super Tucano ba ne) Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sojojin hadin-gwiwa da ke cikin jirage masu saukar ungulu na Mi35 da Mi171 sun bada gudumuwa wajen wannan hari da aka kai wa ‘yan ta’addan.

Daily Post ta rahoto cewa an kai harin saman da ya yi sanadiyyar kashe Umar ne a ranar 14 ga watan Afrilu 2022 a Arinna, karamar hukumar Marte a Borno.

Bin Umar ya nemi ya tsere

An kashe Ammar Bn Umar yayin da yake kokarin tserewa bayan kusan tsawon mako daya ya na gumurzu da dakarun MNJTF da na Operation Desert Sanity.

Kara karanta wannan

Dakarun hadin gwiwa sun yi gagarumin nasara: Sun kashe kwamandojin ISWAP 10 da mayaka 100 a tafkin Chadi

Sojoji sun yi ruwan wuta a Kwalaram, Sabon Tumbun da Jibularam, hakan ta sa ‘yan ta’adda suka fake a yankunan Kwalori, Doron Kirta, Buningyil da L/Libi.

Wasu sojojin ISIS da suka sha da kyar a harin sun tsere zuwa Kirta dauke da kudin da ake zargin su na rabawa ISWAP. Ana tunanin sun fice ta iyakokin Kamaru.

Jirgin sojoji ya yi hadari

A yammacin ranar Talatar nan da wuce ne aka ji labari wani jirgin horar da sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a garin Kaduna, har an rasa rayuka biyu.

Hakan na zuwa ne a lokacin da ake zargin ‘yan ta’addan na kungiyar sun kashe sojoji biyu da ‘yan sanda a harin da suka kai a yankin Molai a wajen Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel