Daga rubutu a Facebook: An kori ma'aikacin gwamnati bisa yada jita-jitar mutuwar gwamnan APC

Daga rubutu a Facebook: An kori ma'aikacin gwamnati bisa yada jita-jitar mutuwar gwamnan APC

  • An dakatar da wani ma’aikacin gwamnati bisa zargin yada labarin karya game da lafiyar gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo
  • A cewar shugaban ma’aikatan jihar, Fasto John Adeyemo, jami’in ya wallafa labarin karya ne a shafin sa na Facebook
  • A halin da ake ciki, Adeyemo ya ce an mika sunan ma’aikacin da ake magana a kai ga hukumar ladabtar da ma’aikata domin samun hukuncin da ya dace da laifinsa

Jihar Ondo - Gwamnatin jihar Ondo ta dakatar da wani ma’aikacin gwamnati bisa zarginsa da yada labaran karya game da mutuwar gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban ma’aikatan, Fasto John Adeyemo wanda bai bayyana sunan ma’aikacin ba ya fada a Akure cewa matakin ladabtarwa ya zama dole ne kan yada jita-jitar mutuwar gwamna da jami'in ya yi.

Kara karanta wannan

Abin kunya: FCDA ta garkame ofisoshin ma'aikatan Gwamnati a Abuja a dalilin taurin-bashi

Adeyemo ya ce an dakatar da ma’aikacin da ake magana a kai tare da mika sunansa ga hukumar ladabtar da ma’aikata domin samun hukuncin da ya dace dashi.

An dakatar da ma'aikaci bisa yada jita-jitar mutuwar gwamna
Baki ke yanka wuya: An kori ma'aikacin gwamnati bisa yada jita-jitar mutuwar gwamnan APC | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Jami’in ya wallafa labarin karya ne a shafinsa na Facebook, wannan mummunar dabi'a ce da ba za a amince da ita ba a gwamnati."

Shugaban ma’aikatan, duk da haka, ya ba da shawarar kakaba takunkumi mai tsauri kan masu yada labaran karya don ya zama darasi ga wasu kasancewar irin wadannan labaran na karya na haifar da matsala a cikin al’umma.

Adeyemo, ya bayyana farin cikinsa da yadda gwamnan ya dawo kasar nan cikin koshin lafiya, yana mai cewa “Allah ya kunyata masu yada jita-jita da masu daukar nauyinsu."

Idan baku manta ba, gwamna Akeredolu ya fara hutun makwanni biyu a matsayin hutun sa na shekara a ranar 1 ga Afrilu, 2022.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Wannan yasa ya mika mulki ga mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa a matsayin mukaddashinsa.

Sai dai kuma a lokacin da Gwamnan baya nan, an yi ta rade-radin cewa ya rasu ne a wani asibitin kasar Jamus, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A halin da ake ciki, da yake jawabi a lokacin da ya dawo jihar, gwamnan ya bayyana wannan jita-jita a matsayin mugun nufi da kirkirarren labari daga 'yan tsagin siyasa.

Akeredolu ya godewa al’ummar jiharsa, inda ya ce yana raye daram kuma zai koma bakin aiki a mako mai zuwa; ranar Litinin mai zuwa.

Kano: Kwamishinan Da Ganduje Ya Ce Kada Ya Ajiye Aiki Ya Bijire Wa Umurnin, Ya Yi Murabus Ya Yi Tafiyarsa

A wani labarin, kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kudi na Jihar Kano, Nura Muhammad Dankadai, ya mika murabus dinsa, sabanin umurnin da Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar ya bada, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilai

Dankadai yana daya daga cikin kwamishinoni uku da Ganduje ya basu umurnin kada su ajiye aikinsu.

Kwamishinoni bakwai ne suka bayyana niyyarsu na ajiye aiki domin za su yi takara a zaben shekarar 2023 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.