Abin kunya: FCDA ta garkame ofisoshin ma'aikatan Gwamnati a Abuja a dalilin taurin-bashi

Abin kunya: FCDA ta garkame ofisoshin ma'aikatan Gwamnati a Abuja a dalilin taurin-bashi

  • Federal Capital Territory Authorities ta ce ta na bin wasu ma’aikatun gwamnatin tarayya tulin bashi
  • Wadannan ma’aikatu da hukumomi sun gagara biyan bashin, a karshe AEPB ta rufe masu ofisoshi
  • Kudin da hukumar ta ke bin ma’aikatun ya haura N10bn, an je har kotu amma abubuwa sun ci tura

Abuja - Hukumar Federal Capital Territory Authorities (FCTA) ta rufe wasu ofisoshin ma’aikatun tarayya a dalilin gaza biyar bashin da yake kan su.

Premium Times ta ce gine-ginen gwamnatin da aka garkame su na da dama. Har zuwa lokacin da mu ka samu rahoton, ba a iya tabbatar da dukkansu ba.

Abin da yake tabbas shi ne a ranar Talata aka shiga rufe wasu ma’aikatun saboda hukumar Abuja Environmental Protection Board ta na bin su bashin kudi.

Kara karanta wannan

Zulum: Muna Sane Da Hatsarin Da Ke Tattare Da Shirin 'Sauya Tunanin Tubabbun Ƴan Ta'adda'

Hukumar AEPB mai kula da birnin tarayya ta biyo ma’aikatun bashin sama da Naira Biliyan 10. Wannan ya sa aka zo da wasu jami’an tsaro, aka datse su.

Vanguard ta ce daga cikin gine-ginen gwamnati da aka rufe akwai na ma’aikatar ayyuka da gidajen tarayya da ke unguwa Mabushi, da ma’aikatar tsaro.

Sai kuma ma’aikatar kiwon lafiya, hukumar daidaito na FCC, da ma’aikatar kasuwanci da hannun jari na tarayya, da kuma ginin ma’aikatar ilmi na kasa.

Hukumar FCDA
Ginin ma'aikatar tsaro (ba nan aka rufe ba) Hoto: hotels.ng
Asali: UGC

Haka zalika an hada da ofishin Nigeria Security and Civil Defence Corps watau NSCDC da ke Wuse. Ba dai iyaka wadannan kurum abin ya shafa ba.

Maganar bashi ta je kotu

Kafin a kai ga rufe ofisoshin ma’aikatun, sai da FCTA ta kai maganar zuwa wani kotu a Wuse, aka kuma bukaci wadanda ake kara su zo su kare kan su.

Kara karanta wannan

Yafewa Nyame da Dariye ta jawo Jami’an EFCC, ICPC su na jifan Shugaban kasa da zargi

Bayan sun gagara kare kan su a gaban Alkali ne sai aka ga Darektan AEPB, Osilama Braimah, ya dauki jami’ai domin a rufe ofisoshin, a hana su yin aiki.

Kudin da suka makale

Ga bashin da ke kan wuyan ma’aikatun tarayya kamar yadda Osilama Braimah ya bayyana a jiya.

Ma’aikatar ayyuka— N9,998,625.00; ma’aikatar tsaro –N17,220,775.00; Hukumar daidaito, FCC—N10,128,906.25; sai Hukumar kason albashi—21,683,750.00.

Hukumar kula da aikin gwamnati–2,451,649.50; ma’aikatar kiwon lafiya—N14,204,843.75; Ma’aikatar kasuwanci—N19,222,287.50; Ma’aikatar ilmi –N25,838,275

A karshe kuma akwai hukumar Nigeria Security and Civil Defence Corps–N16,583,031.25.

Za a magance matsalar tsaro - Buhari

An ji mai magana da yawun shugaban Najeriya, Garba Shehu ya na fadawa Najeriya cewa sojoji za su zo da sababbin dabarun yaki da ‘yan bindiga da 'yan ta'adda.

Malam Garba Shehu ya ce ana kuma fatan ba za a sake sa bam a titin jirgin kasan Kaduna-Abuja ba, sannan ya sha alwashin ceto wadanda ke hannun 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun tsare mai tsohon ciki, ta na kokarin nakuda, su na neman kudin fansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel