Karin bayani: 'Yan bindiga sun farmaki tawagar dan majalisar tarayya a jihar Filato

Karin bayani: 'Yan bindiga sun farmaki tawagar dan majalisar tarayya a jihar Filato

  • Labarin da muke samu daga jihar Filato ya bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun farmaki tawagar dan majalisa
  • Rahotanni sun bayyana cewa, akalla mutane biyu 'yan bindigan suka hallaka yayin mummunan harin
  • Ya zuwa yanzu dai hukumomi basu ce komai a kai ba, amma wata kungiya ta zargi Fulani da aikata mummunan aikin

jihar Filato - Wasu ‘yan bindiga a ranar Talata da daddare sun yi wa tawagar sabon zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa-Bassa, Musa Agah kwanton bauna.

An ce dan majalisar tarayyar da mukarrabansa na dawowa gida ne da misalin karfe 9 na dare a lokacin da lamarin ya faru a kusa da Twin Hill Miango, a karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin ga AIT, hadimin dan majalisar, Moses Maly, wanda suke cikin mota daya lokacin da lamarin ya faru, ya ce matar dan majalisar da ‘ya’yansa biyu su ma suna tare dasu amma duk sun tsere yayin da motarsa ta farfashe da barin harsasai.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige sabon zababben kansilan APC a Katsina, sun yi awon gaba da matansa 2

Mutane biyu sun mutu yayin da wasu ‘yan bindiga suka farmaki ayarin dan majalisar tarayya a Filato
'Yan bindiga sun farmaki tawagar dan majalisar tarayya a jihar filato | Hoto: ait.live
Asali: UGC

Maly ya ce wasu mutane biyu da ke kan babura da suka hada da Shugaban Jam’iyyar PDP na unguwa da Shugabar mata ta PDP da ke gaban ayarin ne suka fara cin karo da ‘yan bindigar, kuma dai an kashe su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwanan nan aka rantsar da Musa Agah a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa-Bassa bayan nasarar da ya samu a zaben maye gurbi na ranar 26 ga watan Fabrairu.

Ba a iya samun jin ta bakin 'yan sanda ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton, haka nan The Nation ta ruwaito.

Hakazalika, wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Irigwe Developement Association (IDA), Danjuma Dickson Auta ya fitar ta tabbatar da faruwar harin, tare da daura alhakin harin kan Fulani mahara a yankin.

Kara karanta wannan

Iftala'i: Bam ya tashi a Taraba, mutane 3 sun mutu, wasu da dama sun jikkata

Daga Zuwa Daurin Aure, Ƴan Bindiga Sun Sace Baƙi Guda 5 a Hanyarsu Ta Komawa Gida

A wani labarin, a kalla mutane biyar ne cikin baki da suke dawowa daga bikin daurin aure na gargajiya a Anambra a daren ranar Litinin ne suka fada hannun yan bindiga, rahoton Daily Trust.

DSP Toochukwu Ikenga, Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Anambra, ya tabbatar da afkuwar wannan lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya a Awka.

The Cable ta rahoto cewa Ikenga ya ce yan sanda sun bazama don ceto wadanda aka sace a kuma sada su da iyalansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.