Al-mundahana: EFCC ta Tsare Ɗan Tsohon Gwamnan Nasarawa kan wasu Kudade N130m
- Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, an tsare dan tsohon gwamnan jihar Nasarawa Tanko Al-Makura
- An ce an tsare Amir Al-Makura ne saboda zarginsa da sayen wata kadara da kudin da ba a san asalinsu ba
- Wannan lamari dai na zuwa ne watanni tara bayan kama tsohon gwamnan da matarsa kan zargin rashawa
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta titsiye wani dan tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura bisa zargin sayan kadara ta Naira miliyan 130.
Majiyoyi daga hukumar da suka samu bayanai kan lamarin amma aka hana su shaida wa manema labarai, sun ce Amir Al-Makura mai shekaru 24, ya biya tsabar kudi Naira miliyan 96 “da kudin kasashen waje” a matsayin kudin wani bangare na kadarar.
A cewar majiyar ga jaridar Premium Times:
“A ci gaba da binciken mu na harkar kadarori, mun gayyaci Amir Tanko Al-Makura dan Sanata Al-Makura.
“Wanda ake zargin dan shekara 24 ne kuma ya sayi gida a Bilaad Realty Ltd akan kudi N130,000,000.00 kuma ya biya kudi a hannu har N96,000,000.00 a kudin kasashen waje.”
Majiyar ta ce Amir ya je ga hukumar “amma ya kasa yin bayanin inda aka samu kudin ko kuma bayar da cikakken bayani kan yadda aka samu kudin.”
Majiyar ta ce har yanzu wanda ake zargin yana tsare domin har yanzu bai cika sharuddan belin da aka gindaya masa ba.
Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna Da Matarsa Kan Zargin Rashawa
Kafin kama Amir Al-Makura, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma sanata mai ci a yanzu, Tanko Al-Makura da matarsa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Majiyoyi daga hukumar yaki da rashawar sun shaidawa Premium Times cewa a halin yanzu jami'an EFCC na yi wa tsohon gwamnan da matarsa tambayoyi a hedkwatar ta da ke Abuja.
Duk da cewa ba a samu cikaken bayani kan dalilin kama tsohon gwamnan da matarsa ba, majiyoyi sun ce kamun na da nasaba da zargin cin amana da bannatar da kudade da gwamnan yayi yayin mulkinsa na shekaru takwas a matsayin gwamnan Nasarawa.
Al-Makura ya rike mukamin gwamnan Nasarawa daga 2011 zuwa 2019 kafin aka zabe shi a matsayin sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu a jihar.
Da aka tuntube shi game da batun, kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya ce kawo yanzu ba a masa bayani a kan lamarin ba.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Janar din Sojan Bogi kan damfarar miliyoyi
A wani labarin daban, hukumar EFCC reshen jihar Legas ranar Litinin, 11 ga watan Afrilu, 2022 ta gurfanar da Bolarin Abiodun wani janar din sojin kasa na bogi a gaban mai shari’a Oluwatoyin Taiwo na kotu ta musamman dake Ikeja, Legas.
Bolarin ya gurfana ne kan tuhume-tuhume goma sha uku wanda suka hada da zamba, karya da samar da takardun bogi da yaudara ta kudi nera miliyan dari biyu da sittin da shida da dari biyar.
Hukumar ta bayyana hakan ne a jawabin da ta fitar ranar Litinin, 11 ga Afrilu, 2022.
Asali: Legit.ng