Hukumar zaɓe INEC ta yi magana kan yawan mutanen dake neman takarar shugaban kasa a 2023

Hukumar zaɓe INEC ta yi magana kan yawan mutanen dake neman takarar shugaban kasa a 2023

  • Hukumar zaɓe INEC ta ce ko kaɗan ba ta damu da yawan yan takarar dake neman shugaban ƙasa ba a zaɓen 2023
  • A cewar hukumar mai zaman kanta, jam'iyyun siyasa 18 ne halastattu, dan haka su ne kaɗai zasu gabatar mata da yan takarar su
  • INEC ta ce yawan yan takara ya shafi jam'iyyun siyasa domin su ke da alhakin gudanar da zaɓen fidda gwani

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa, (INEC), ta ce ƙaruwar mutanen dake nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 be dame ta ba.

INEC ta ce jam'iyyun siyasa 18 ne kacal halastattun da za su gabatar mata da yan takarar su a tseren kujera mai daraja ta ɗaya a Najeriya, kuma kowace jam'iyya ɗan takara ɗaya zata tsayar.

Kara karanta wannan

2023: Abu ɗaya zai kawo karshen yan bindiga a Najeriya, Gwamnan dake son gaje Buhari ya gano

Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC.
Hukumar zaɓe INEC ta yi magana kan yawan mutanen dake neman takarar shugaban kasa a 2023 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A wata hira da jaridar Leadeship a Abuja ranar Lahadi, Sakataren watsa labarai na shugaban INEC ta ƙasa, Rotimi Oyekanmi, ya ce:

"Jam'iyyun siyasa 18 ne kaɗai zasu gudanar da zaɓen fidda gwani, dan haka su kaɗai hukumar zata sanya wa ido."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aikin jam'iyya ne shirya zaben fidda gwani - INEC

Oyekanmi ya bayyana cewa jam'iyyun siyasa ne ke da nauyin shiryawa da gudanar da zaben fitar da ɗan takara bisa tanade-tanaden dokokin zaɓe da tsarin jadawalin INEC.

"Saboda haka, idan masu neman kujerar shugaban ƙasa suna da yawa, ya wajaba kan jam'iyyun su na siyasa su bi matakan tsayar da mutum ɗaya, dan haka abun yana kan su ne."
"Mun yi shirin sa ido a zaɓen fidda gwani 18 ko abin da bai kai haka ba, ya danganta da jam'iyyun da suka sanar da mu za su gudanar da zaben cikin lokacin da aka ƙayyade."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda 'Yan Bindiga Suka Ci Karen Su Ba Babbaka, Suka Halaka Ma'aikacin INEC a Wurin Aikin Rijistar Zaɓe

Ya ƙara da bayanin cewa alhakin hukumar INEC ne da sa io domin tabbatar da jam'iyyu sun bi matakan ta hanyar da doka ta tanada.

A wani labarin kuma bincike ya nuna Yadda yaƙin Rasha da Ukaraine ya yi mugun tasiri kan farashin kayan Gine-Gine a Najeriya

Masana sun koka kan yadda farashin kayayyakin amfani wajen gine-gine suka tashi tun bayan fara yaƙin Rasha da Ukraniya.

A cewarsu, ya kamata gwamnatin tarayya ta sake gyara a kasafin 2022 duba da Farashin kayayyaki a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel