2023: Abu Ɗaya 'Yan Najeriya Zasu Yi Su Kawo Karshen Yan Bindiga, Gwamna Wike na PDP

2023: Abu Ɗaya 'Yan Najeriya Zasu Yi Su Kawo Karshen Yan Bindiga, Gwamna Wike na PDP

  • Gwamna Wike na jihar Ribas ya ce sai yan Najeriya sun kawar da APC tare da maye gurbinta da PDP sannan zasu samu zaman lafiya
  • A cewar gwamnan kafin zuwan APC, mutanen Najeriya ba su san matsalar yan fashin daji ba, jam'iyyar ta zo da su
  • Ya ce shi kaɗai ya rage a Najeriya da zai iya share dattin da jam'iyya mai mulki APC ta shafa wa ƙasar nan

Plateau - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, ya ce yan Najeriya ke da wuƙa da nama wajen kawo ƙarshen ayyukan yan bindiga.

Daily Trust ta rahoto cewa Wike ya ce abu ɗaya da zai kawo ƙarshen ta'addancin yan bindiga shi ne kawar da jam'iyyar APC daga kan madafun iko tare da maye gurbinta da PDP.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Yanzu dai 'yan Najeriya sun fahimci PDP ce gatansu, in ji Sule Lamido

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
2023: Abu Ɗaya 'Yan Najeriya Zasu Yi Su Kawo Karshen Yan Bindiga, Gwamna Wike na PDP Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamna Wike ya yi wannan furucin ne a Jos, babban birnin jihar Filato, sa'ilin da ya ke jawabi ga Deleget ɗin PDP na jihar.

Ya ce:

"Ba wanda ya san ayyukan yan fashin daji sai da APC ta karɓi Najeriya. Jam'iyya mai mulki ce ta haifar mana da yan bindiga, kuma tun daga lokacin muka rasa zaman lafiya a Najeriya."
"Babban aiki kwara ɗaya tal da APC ta yi a jihar Filato shi ne ta'addancin yan fashin daji da kashe-kashe. Kullum abu ɗaya kake ji, an kashe mutum 10, 20, 30, 100 a Filato. Abun takaici ne ba zamu amince da shi ba."

Meya kai Wike jihar Filato?

Daga nan sai ya yi kira ga al'ummar jihar su tabbata jam'iyyar PDP ta koma kan madafun iko a 2023 domin ceto jihar daga rugujewa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda 'Yan Bindiga Suka Ci Karen Su Ba Babbaka, Suka Halaka Ma'aikacin INEC a Wurin Aikin Rijistar Zaɓe

Gwamnan ya kuma gaya wa Deleget cewa ya zo ziyara Filato ne domin sanar musu da niyyarsa ta neman takarar shugaban ƙasa a 2023.

Ya jaddada cewa shi ne kaɗai mutumin da ya rage, wanda zai iya share dukkan dattin da jam'iyyar APC ta kawo wa ƙasar nan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin kuma Atiku Abubakar ya ɗaukar wa yan Najeriya, musamman matasa alƙawari biyu da zaran ya zama shugaban ƙasa a 2023

Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar PDP ya sha alwashin kewaye gwamnatinsa da matasa idan yan Najeriya suka ba shi dama.

Atiku Abubakar ya kuma ƙara da ɗaukar alƙawarin mika mulki ga matasa da zaran ya gama wa'adinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel