2023: Zan miƙa wa Matashi mulki bayan na gama wa'adina, inji Atiku

2023: Zan miƙa wa Matashi mulki bayan na gama wa'adina, inji Atiku

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar PDP ya sha alwashin kewaye gwamnatinsa da matasa idan yan Najeriya suka ba shi dama
  • Atiku Abubakar ya kuma ƙara da ɗaukar alƙawarin mika mulki ga matasa da zaran ya gama wa'adinsa
  • Tsohon mataimakin shugaban ya ɗauki waɗan nan alkawurra ne a wurin taronsa da kungiyoyin magoya baya sama da 200

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ɗauki alƙawarin miƙa mulkin Najeriya hannun matasa idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa kuma da matasa zai cika gwamnatinsa.

Ya yi wannan alƙwarin ne a wurin taronsa da shugabannin kungiyoyi sama da 200 dake goyon bayansa da jagororin TeeCom na faɗin ƙasa a Abuja, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan APC ya gana da Buhari, ya faɗa masa aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa a 2023

A wata sanarwa mai taken, "Atiku zai yi aiki da matasa kuma ya basu mulki, inji kungiyar magoya baya."

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
2023: Zan miƙa wa Matashi mulki bayan na gama wa'adina, inji Atiku Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna jin daɗinsa ganin yadda Matasa suka fito ake damawa da su a siyasa, inda ya ce zai horad da su daga baya kuma ya miƙa musu ragamar tsarin siyasa.

A jawabinsa, an jiyo Atiku na cewa:

"Zan horad da ku siyasa kuma na miƙa muku ragamar mulki. Ina son yin aiki da matasa kewaye da ni saboda matasa na da tunanin sabon abu, kuma sun san cigaban zamani da ƙalubale."
"Dan haka gwamnatin mu zata kasance tana kokarin miƙa mulki daga waɗan da suka ga jiya suka ga yau zuwa matasan zamani."

Matasa zasu dama a mulkin Atiku

Ƙungiyar magoya bayan Atikun ta roki matasa su zaɓi Atiku, a cewarta za su samu damarmaki sosai ƙarƙashin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Idan ban gyara Najeriya a shekara ɗaya ba ku mun kiranye, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki dama a 2023

Wani sashin sanarwan kungiyar ya ce:

"Mai girma Atiku Abubakar ya shirya kuma yana da burin aiki tare da matasa kuma ya ba su mulki, wannan hanya ce mikakka da matasa za su shiga harkokin mulki domin zamanantar da Najeriya."

A wani labarin kuma Babbar Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar PDP saboda wani kuskure ɗaya da ya tafka kafin a zaɓe shi

Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a birnin Abuja ta tsige Tochukwu Okorie daga matsayin shugaban PDP a jihar Ebonyi.

Alƙalin Kotun ya kafa hujja da cewa Okorie bai maida Fam ɗin takara a lokacin da PDP ta ɗibar masa ba, dan haka bai cancanta ya shiga zaɓe ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel