Hotunan kyawawan 'yan 3 da ke soyayya da saurayi 1, sun ce suna shirin aurensa

Hotunan kyawawan 'yan 3 da ke soyayya da saurayi 1, sun ce suna shirin aurensa

  • Evelyn Wanjiru, Mary Muthoni da Catherine Wanjiru 'yan uku ne a kasar Kenya, wadanda suka tsunduma a soyayyar namiji daya
  • 'Yan ukun masu kama daya sun bayyana yadda suke soyayya da Big Man Stivo, saboda suna da ra'ayi iri daya
  • Mary ta bada labarin yadda duk da komai tare suke, sannan suna sabawa da mutumin, suka shirya aure dashi

Yayin da auren mutum daya da 'yan biyu masu kama daya yazo wa mutane da dama a abin al'ajabi, 'yan uku daga Kenya na shirin rayuwa da miji daya.

Labarin Eve, Mary da Cate na da ban sha'awa. Suna matukar kama da juna, sannan wani abun burgewa, suna da ra'ayi daya.

Hotunan kyawawan 'yan 3 da ke soyayya da saurayi 1, sun ce suna shirin aurensa
Hotunan kyawawan 'yan 3 da ke soyayya da saurayi 1, sun ce suna shirin aurensa. Hoto daga Mary.
Asali: UGC

'Yan ukun masu kama da juna sun bayyana yadda suke soyayya da mutum daya, wanda ya fada tarkon soyayyarsu a wurare daban-daban.

Kara karanta wannan

Dan majalisa a Filato: An kashe makusantana fiye da 50 a harin 'yan bindiga

Yayin zantawa da wani makusancinsu wanda yayi fice a kasar Kenya, sun ce suna farincikin yadda suke soyayya da mutum daya, saboda yana basu so da kulawa iri daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"In dai yana nuna mana kauna ba tare da bambamci ba, bamu da wata matsala," Mary ta shaidawa Brian Ajon.

Yayin fara soyayya da masoyinmu, Mary ta bayyana cewa Cate ce ta fara haduwa da abokin rayuwarmu, sai dai yayin da ta labartawa sauran, dukkansu suka ce saurayin ya burgesu.

"Cate ta ganshi, sannan ta bamu labarin shi, mu kuma duka muka fara son shi," a cewar Mary.
"Bama da isashshen lokaci yawancin karshen makwanninmu, amma a kalla yana haduwa da ko waccenmu daban-daban, gami da bamu kulawa.
Ta kara da cewa, "Yana haduwa da Mary a ranar Litinin, Eve ranar Talata sannan Cate ranar Laraba."

Kara karanta wannan

Yadda kanin mijina ya babbaka mijina, Mai juna biyu ta bada labari mai ban tausayi a bidiyo

Kyawawan 'yan ukun sun ce sun dauki tsawon shekara daya da rabi suna soyayya da mutumin, sannan suna shirye-shiryen aurensu dashi.

Matashi a Kano,Tijjani, ya sha fiya-fiya bayan samun labarin budurwarsa zata auri maikudi

A wani labari na daban, wani matashi a jihar Kano masi suna Tijjani Abubakar ya yi yunkurin hallaka kansa ta hanyar shan ruwan fiya-fiya ranar Talata, 15 ga watan Febrairu, 2022. Tijjani, dan unguwar Gama a karamar hukumar Nasarawa ta jihar ya tsallake rijiya da baya.

City & Crime ta ruwaito cewa Tijjani ya yi kokarin hallaka kansa ne bayan budurwsa ta jizgashi don auren wani mutumi, wanda yafi kudi da iya soyayya.

DailyTrust ta ce wani mai idon shaida yace Abubakar mai sana'ar sayar da waya ne a Farm Center, ya sha da kyar bayan dan'uwansa ya gansa yana shan fiya-fiyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel