Ba A Yi Sulhu Da ASUU Ba, NASU Da SSANU Za Su Tsinduma Yajin Aiki Na Sai Baba Ta Gani

Ba A Yi Sulhu Da ASUU Ba, NASU Da SSANU Za Su Tsinduma Yajin Aiki Na Sai Baba Ta Gani

  • Kwamitin Hadin Gwiwa (JAC) na Kungiyar ma’aikatan ilimi da cibiyoyi makamantansu marasa koyarwa (NASU) da Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU), ta bayyana shirinsu na fara yajin aiki
  • Ba ta sanya lokacin da za su dawo daga yajin aikin ba, kuma a cewarta hakan ya biyo bayan yadda Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta nuna musu halin ko in kula ne duk da yarjejeniyar da suka yi a baya
  • Kakakin JAC Peters Adeyemi, ya nuna takaicinsu akan yadda gwamnati ta ki gayyatar shugabanninsu don su zauna da su bayan sun kara ba gwamnati makwanni 2 don ta yunkura amma duk da haka babu alamar za ta yi wani abu

Abuja - Kwamitin Hadin Gwiwa (JAC) ta Kungiyar Ma’aikatan Ilimi da Cibiyoyi makamantansu (NASU) da kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU), ta bayyana yadda suka shirya tsaf wurin datse duk ayyukansu a jami’o’i da cibiyoyin ilimi da ke fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Najeriya na matukar bukatar na mulke ta saboda wasu dalilai da ke kasa

JAC ta nuna alhininta akan yadda gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta wofantar da yarjejeniyar da ta yi da kungiyar akan harkar ilimin kasar nan, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Ba A Yi Sulhu Da ASUU Ba, NASU Da SSANU Za Su Fara Yajin Aiki Na Sai Baba Ta Gani
NASU Da SSANU Za Su Fara Yajin Aiki Na Sai Baba Ta Gani. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Twitter

Kakakin JAC ya ce gwamnati ta ki mayar da hankali akan harkokin ilimi

Kakakin JAC, Kwamared Paters Adeyemi wanda ya tattauna da manema labarai a Abuja ya bayyana cewa:

“Sakamakon yadda gwamnati ta ke nuna halin ko-in-kula ga mambobinmu yasa muka yanke shawarar tafiya yajin aiki. Gwamnati ta ki gayyatar shugabancin kungiyarmu don zama da su duk da yadda muka kara makwanni biyu kafin mu yanke shawarar tafiya yajin aikin sai baba ta gani.
“A yau dinnan, makwanni biyun da aka kara sun kai tsakiya kuma gwamnati ba ta ce komai ba, don haka ba mu da wani zabin da ya wuce mu tafi yajin aiki wanda babu ranar komawa.”

Kara karanta wannan

ASUU ta zargi NITDA da Dr. Isa Pantami da kawo siyasa a yajin-aikin da ake yi a Jami'o'i

Adeyemi ya ci gaba da cewa:

“Idan ba a manta ba, Kwamitin Hadin Gwiwar NASU da SSANU ta fara yajin aiki a ranar Juma’a, 5 ga watan Fabrairun 2021 kuma ta sanya hannu a takardar daukar mataki a ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairun 2021. Daga nan muka fara yajin aiki na makwanni biyu inda muka sanya hannu a yarjejeniya ranar Talata, 20 ga watan Oktoban 2020.”

Adeyemi ya bayyana dalilansu na tafiya yajin aikin

Ya ci gaba da bayyana yadda suka sanya hannu a takarda a watan Fabrairun 2021 wacce daga nan suka tafi yajin aikin watan Maris din 2022. Kuma tun yarjejeniyar 2017 da 2018 aka dinga jan zare da tsawo har suka zauna da gwamnati inda suka samu matsaya a 2020 da 2021, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A cewarsa, gwamnati ba ta bar musu wani zabi ba face na daukar mataki, wanda shi ne yajin aiki. Kuma abin ban kunya da takaici shi ne yadda gwamnati ta kasa gayyatar kungiyoyin don su zauna.

Kara karanta wannan

Yadda za a gwabza wajen zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC

Dangane da dalilansu na tafiya yajin aiki, Kwamared Adeyemi ya lissafo abubuwa kamar matsalar biyan albashi ta IPPIS wanda yake kwan-gaba kwan-baya, rashin biyan alawus, rashin samar wa jami’o’i kudaden da suka dace, daukar lokaci mai tsayi don zama a tattauna akan yarjejeniyar 2009 da sauransu.

Yajin Aikin ASUU: Ba Za Mu Bar Titunan Abuja Ba Har Sai An Buɗe Makarantu, 'Kungiyar NANS

A bangare guda, Kungiyar Daliban Najeriya, NANS, a ranar Litinin ta cigaba da zanga-zangar ta na neman ganin an kawo karshen yakin aikin da kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ke yi.

Da ya ke magana a yayin zanga-zangar a Abuja, shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon, ya ce daliban a shirye suke su fito su mamaye manyan titunan Abuja, rahoton The Punch.

Ya kara da cewa daliban sun gaji kuma ba za su fasa abin da suka fara ba har zai an bude dukkan jami'o'i a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel