Shirin zaben 2023: An samu nakasu a 45% na rajistar zabe a Najeriya, inji INEC

Shirin zaben 2023: An samu nakasu a 45% na rajistar zabe a Najeriya, inji INEC

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta nuna damuwa kan samun rajistar zabe marasa aiki da inganci daga 'yan Najeriya
  • Hukumar ta fitar da alkaluma, inda tace akalla kashi 45% cikin dari na rajistar zabe a kasar suna nakasu
  • Hakazalika, ta fitar da adadin katunan zaben PVC da ake dasu a kasa, kana za a fara mika su ga jihohin kasar

Yayin da ake ci gaba da shirin zaben 2023, hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar sabon rahoton adadin katunan zabe da adadin rajistar zabe a Najeriya, inda INEC tace akalla kashi 45% ne aka gano suna da nakasu.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ta INEC ta bayyana dalla-dalla adadin wadanda suka yi rajistar zabe, da kuma shirin da take na fara rarraba katunan a fadin Najeriya nan kusa.

Kara karanta wannan

Zaben kananan hukumomin Katsina: APC ta lallasa PDP, ta lashe dukka kujeru 31

Batun katunan zabe gabanin zaben 2023
Shirin zaben 2023: An samu nakasu a 45% na rajistar zabe a Najeriya, inji INEC | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

INEC ta ce, ya zuwa ranar 14 ga watan Janairun 2022, akalla katunan zabe 1,390,519 ke da rajista ingantacce a Najeriya, inda ta bayyana cewa, za ta ci gaba da tantance rajistar sauran katunan zabe a Najeriya.

Wata sanarwar da hukumar ta INEC ta fitar a yau dinnan ta shafin Facebook, wanda Legit.ng Hausa ta gano ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Abin takaici, har yanzu batun nakasu a rajista yana ci gaba da wanzuwa wanda muka gano yayin tantance sabbin bayanan rajista."

Hukumar ta bayyana cewa, ta bullo da sabon tsarin tantance rajistar katunan zabe, kuma tanan ta gano duk wasu kalubale da ke tattare da rajistar wasu katunan.

A cewarta:

"A halin yanzu, kusan kashi 45% na rajistar da aka kammala a duk fadin kasar na da nakasu, wanda ya kai kashi 60% ko fiye a wasu Jihohi. Wannan dirkaniyar ta faru a duk Jihohin Tarayyar kasar nan. Babu wata Jiha da ta tsira daga gare ta.

Kara karanta wannan

Ya bayyana: Adadin Mata, Maza da Yaran da yan bindigan suka sace a harin jirgin Abuja-Kaduna

"Ba za a saka wadannan katuna marasa inganci a cikin jerin Rajistan Masu Zabe ba. A kudurinmu na tabbatar da gaskiya, za a gabatar muku da rabon alkaluman rijistar da suka hada da kaso na rijista masu aiki da kuma wadanda suke da nakasu na kowace jiha, a wannan taron manema labaran.
Za a daura wannan bayanin a shafin yanar gizon hukumar da kuma shafukan sada zumunta nan da nan."

Matar gwamnan APC ta shiga jerin 'yan takarar sanata a jiharsu

A wani labarin, rahoton Daily Trust ya bayyana cewa, matar gwamnan jihar Ondo, Mrs. Betty Anyanwu-Akeredolu, ta shiga tseren takarar Sanata a zaben 2023.

Da take yiwa manema labarai jawabi a Owerri, babban birnin jihar Imo, a ranar Juma’a, Uwargidan gwamnan Ondo ta ce tana da sha’awar wakiltar mazabar Imo ta Gabas saboda tana son kawo sauyi a yankin.

A halin yanzu dai Sanata Onyewuchi Francis Ezenwa na jam'iyyar PDP ne ke wakiltar gundumar a zauren majalisar dokoki ta kasa.

Kara karanta wannan

Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamun daukaka ne, In ji dan majalisa daga arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.