Hasashe mai daukar hankali: Musulmai za su azumci Ramadana sau biyu a 2030

Hasashe mai daukar hankali: Musulmai za su azumci Ramadana sau biyu a 2030

  • Wani rahoton hasashe da jaridun kasashen Larabawa suka fitar ya bayyana yadda za a samu sauyin yin azumin Ramadana
  • Wannan sauyi zai faru ne bisa sauyin yanayi kamar yadda masana ilimin taurari suka hango inji rahoton
  • A shekarar 2030, ana kyautata zaton za a yi azumin Ramadana sau biyu a cikinsa, bisa hangen masana ilimin taurari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Dubai, Daular Larabawa - Jaridar Arab News ta tattaro cewa, musulmai za su yi azumin Ramadana sau biyu a shekara ta 2030, kamar yadda wasu masana ilmin taurari suka yi hasashen.

Masana sun ce watan azumi zai shigo sau biyu a wannan shekara ta 2030, na farko a watan Janairu, sannan kuma a karshen watan Disamba, lamarin da ya taba faruwa a shekarar 1997.

Dalilin da ke tattare da haka ya ta’allaka ne da bambamcin da ke akwai tsakanin Kalandar Hijira, wanda ya ginu a kan zagayowar wata, da kalandar Miladiya da ke tafiya da zagayawar duniya a gefen rana.

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta nemi a kame dan fafutukar raba Najeriya gida biyu

Yadda za a azumci Ramadana sau biyu
Hasashe mai daukar hankali: Musulmai za su azumci Ramadana sau biyu a 2030 | Hoto: arabnews.com
Asali: UGC

Lamarin dai yana faruwa ne kusan duk bayan shekaru 30 saboda kalandar Hijira na da nakasun kwanaki 11 idan aka kwatanta da na Miladiyya, inji masanin taurarin Saudiyya Khaled al-Zaqaq a wani rubutu a shafinsa na Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikakkiyar shekara a kalandar Hijira kan dauki kwanaki 354, sabanin kwanaki 365 da ke cikin kalandar Miladiyya.

Yaushe za a yi azumi sau biyu a 2030?

A shekarar Hijira ta 1451, watan Ramadan zai fara ne kusan 5 ga Janairu, 2030, yayin da a shekara ta 1452 bayan hijira zai zo ne a kusan 26 ga Disamba, 2030, kamar yadda Al-Arabiya ta tattaro.

Hakan na kuma nufin cewa Ramadana na fadowa a yanayi daban-daban kowace shekara - yin Ramadana a yanayi iri guda na zagayowa ne kusan shekaru 32.

Ramadana a shekarar 1449 bayan Hijira, wanda zai fara a 2028, zai gudana ne a tsakiyar hunturu.

Kara karanta wannan

Dangi sun shiga makoki yayin da tuwo ya kashe mutum, aka kwantar da 4 a asibiti

A shekara ta 1466 bayan hijira, daidai da shekara ta 2044, watan mai alfarma ya kamata ya fara ne a lokacin bazara.

Ramadan 2022: Saukakan hanyoyin nema da gane daren Lailatul Qadari

A wani labarin, daren Lailatul Qadari, dare mafi daraja daga cikin darare, dare ne da Allah Madaukakin Sarki ya saukar da Al-Kur'ani; littafin da aka saukarwa Annabi Muhammad (SAW).

Duk wata ibadar da ake yi a cikin wannan dare guda na daidai da shekaru 84 na ibada a wajen wannan dare, a cewar rawayoyi da dama, kamar yadda WhyIslam.org ta tattaro.

A cikin Al-Kur'ani, suratul Qadr, Allah SWT ya yi bayani kan falalar da ke tattare da daren, inda yace daren Lailatul Qadari daidai yake da falalar darare 1000 na sauran darare, kana mala'iku na saukowa a wannan dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.