Ramadann 2022: Saukakan hanyoyin nema da gane daren Lailatul Qadari

Ramadann 2022: Saukakan hanyoyin nema da gane daren Lailatul Qadari

  • Ya zuwa yanzu, akalla an yi azumi 10 daga cikin 30 ko 29 na watan Ramadana a Najeriya a shekarar 2022
  • Musulmi za su fara duba daren Lailatul Qadari, domin gamo da katar kan falalar da ke kunshe a cikinsa
  • Mun tattaro muku hanyoyin da ake bi wajen gane alamomi da kuma duban daren na Lailatul Qadari

Daren Lailatul Qadari, dare mafi daraja daga cikin darare, dare ne da Allah Madaukakin Sarki ya saukar da Al-Kur'ani; littafin da aka saukarwa Annabi Muhammad (SAW).

Duk wata ibadar da ake yi a cikin wannan dare guda na daidai da shekaru 84 na ibada a wajen wannan dare, a cewar rawayoyi da dama, kamar yadda WhyIslam.org ta tattaro.

Hanyoyin gane daren Lailatul Qadar
Ramadann 2022: Saukakan hanyoyin neman daren Lailatul Qadari | Hoto: GettyImages
Asali: UGC

A cikin Al-Kur'ani, suratul Qadr, Allah SWT ya yi bayani kan falalar da ke tattare da daren, inda yace daren Lailatul Qadari daidai yake da falalar darare 1000 na sauran darare, kana mala'iku na saukowa a wannan dare.

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Azumi Cikin Tsananin Zafi, Tare da Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Wanna dare mai daraja yana fadowa ne a daya daga cikin darare goma na karshen watan Ramadan.

Wani Hadithin da Imam Bukhari da Imam Muslim suka ruwaito a littafansu yana cewa:

"Duk wanda ya sallaci daren Lailatul Kadari yana mai imani da ikhlasi, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa"

Neman Daren Lailatul Qadri

Annabi Muhammad (SAW) ya kwadaitar da neman daren Lailatul-kadri kuma tsawon shekaru, musulmi a fadin duniya suna ta kokarin yin hakan a kowane wata na Ramadana.

Don taimakawa musulmi wajen neman wannan dare na musamman mai daraja, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba da wasu alamu na gane yanayin daren.

Daya daga ciki shi ne dare zai fado a wani dare mai ban mamaki cikin dararen wutiri na goman karshe a Ramadana.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malaysia za ta daure ko cin tarar 'yan kasa da ke cin abinci da rana a Ramadan

Lailatul-Qadr: Ta yaya kuke tantance dararen wutiri na karshen Ramadana

Shakiel Humayun a cikin wani sako da AboutIslam.net ya wallafa ya bayyana cewa ganin daren na Lailatul Qadari a daren wutiri ba lallai ba ne ya fado a kwanakin wata na wutiri ba.

A cewarsa cewa daren Lailatul-kadri zai fado ne a cikin wani dare mai ban mamaki a goman karshe na watan Ramadan, ba daidai yake da cewa zai fada kan daya daga cikin dararen wutiri kai tsaye ba.

“Watannin hijira na iya zama kwanaki 29 ko 30, gwargwadon ganin wata, idan wata ya kare yana da kwana 30, dararen wutiri za su iya fadowa akan tagwayen darare."

Laylatul-kadri: Hanyar kirge don gano daren Lailatul Qadari

Annabi SAW ya ba da wani haske a cikin wani Hadithi game da wannan batu, inda yake cewa:

"Ku neme shi (Lailatul kadari) a goman karshe na Ramadan, a 9 na karshe, a 7 na karhs, a 5 na karshe."

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi

- Al-Bukhari

Idan aka yi la’akari da abin da ya gabata, idan Ramadan yana da kwanaki 30, to darare 9 da suka rage a wata su ne 22 ga Ramadan da kuma dararen da ke bayansa; 24, 26, 28 da 30.

Don haka dararen da za a nema su ne sauran darare na wutiri, wato dare na 9, da na 7, da na 5, da na 3, da na karshe.

Wadannan darare za su yi daidai da 22 ga Ramadan, 24 ga Ramadan, 26 ga Ramadan, 28 ga Ramadan da 30 ga Ramadan.

Ko da yake duk wadannan ranaku duka ranaku ne tagwaye, amma a lokaci guda, darare ne na wutiri dangane lissafin adadin dararen da suka rage na watan.

Idan Ramadan ya zo da kwanaki 29, dare na 9 ya zama 21 ga Ramadan, sauran dare na 7 kuma shi ne na 23, 5 kuma ya zama 25, da sauransu.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Ramadaniyyat 1443: Adalcin Shaikhul Islam Ibn Taimiyya (RH), Sheikh Dr Sani Rijiyar Lemo

A wani rahoton da muka hada muku, Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo malami ne a tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar Bayero da Kano kuma shugaban cibiyar nazarin addinai a jami'ar.

Wannan karo, Malam ya yi magana da daya daga cikin Manyan Maluman addinin Musulunci magabata.

Ҝungiyar Mu'utazilawa, ƙungiya ce ta 'yan bidi'a. Ta bayyana ƙarshe-ƙarshen daular Banu Umayya, sannan ta bunƙasa a zamanin daular Abbasiyya. Wani almajirin Al-Hasanul Basari, mai suna Wasilu ɗan Aɗa' (80-130) shi ne ya dasa dashenta na farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel