Jerin rukunin mutane 4 da ke takaicin bayyanar burin Osinbajo na gaje Buhari

Jerin rukunin mutane 4 da ke takaicin bayyanar burin Osinbajo na gaje Buhari

Wasu 'yan Najeriya ba su yi farincikin bayyana bukatar shugabancin kasa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi a ranar 11 ga watan Afirulun 2022.

Mutane da dama ba su yi farin ciki bane saboda kungiyoyin siyasansu ko kuma wasu abubuwa da suka yi imani dasu.

Jerin rukunin mutane 4 da ke takaicin bayyanar burin Osinbajo na gaje Buhari
Jerin rukunin mutane 4 da ke takaicin bayyanar burin Osinbajo na gaje Buhari. Hoto daga @ProfOsinbajo
Asali: Facebook

Masu kiyasi sun ce takarar Farfesa Yemi Osinbajo zata raba kawunan gwamnonin Kudu maso yamma da na jam'iyya mai mulki APC, musamman damar samar da shugaban kasa daga kudu.

Daga martanin mutane a kafafan sada zumuntar zamani, za a iya gano yadda mutane da dama ba su yi farin cikin da bayyana bukatar Osinbajo ba.

Ga irin mutanen da ke kalubalantar bukatarsa.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

1. Magoya bayan Asiwaja Ahmed Tinubu.

2. 'Yan Najeriyan da sukayi imani da cewa mataimakin shugaban kasan bai cancanta ba.

3.Magoya bayan 'yan takarkarin kudu maso gabas.

4. Wadanda ke kallon Osinbajo a matsayin wanda ke bayyana addininsa.

Jerin mutanen da ke farinciki da bayyana bukatar zama shugaban kasa da Osinbajo ya yi

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana bukatar zama shugaban kasa a shekarar 2023, a ranar Litinin, 11 ga watan Afirilu. Nuna bukatar da ya yi ya matukar faranta zukatan wasu mutane. Wanda hakan ya kawo karshen jita-jitan da aka dau tsawon watanni anayi akan bukatarsa na takarar shugaban kasa a 2023, sannan ya ba wa wasu 'yan takara damar neman kujerar. Haka zalika, ya sanya shi yin fito na fito da tsohon ubangidansa na jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya nuna bukatarsa a farkon shekarar.

Jiga-jigan jihohi uku na kudu maso yamma wadanda Osinbajo zai iya rasa kuri'unsu idan ya zama 'dan takarar jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Sai dai kai ka zo: Tinubu ya tura gayyata ga gwamnonin APC, suka ki amsa gayyatarsa

Wannan na nuna cewa akwai bada kala yayin zaben cikin gidan jam'iyyar APC idan ta tashi zaben 'dan takarar shugaban kasa.

Bayyana bukatar da Osinbajo ya yi na nufin yin fito na fito da tsohon ubangidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ya ce ya dade yana burin zama shugaban kasa.

Yadda na zama mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bada labari mai taba zuciya a bidiyo

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a watan Disamban 2021 ya yi magana kan yadda ya zama mataimakin shugaban kasa a APC a 2015.

Bidiyon da ya saki ya bayyana a watan Janairu a Twitter yayin da ake ta rade-radin cewa Osinbajo na son gaje kujerar Ubangidansa Buhari a 2023, faston kuma farfesan shari'ar ya alakanta zamansa mataimakin shugaban kasa da ikon Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel