Sai da nemi kujerar gwamna sau 4 kafin na yi nasara a 1999, Atiku Abubakar

Sai da nemi kujerar gwamna sau 4 kafin na yi nasara a 1999, Atiku Abubakar

  • Mai niyyar zama shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya shawarci matasa su kasance masu jajircewa a siyasa
  • Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa sai da nemi kujerar gwamna sau hudu kafin yayi nasara
  • A shekarar 2019, Atiku ya samu kuri'u milyan goma da daya inda Shugaba Buhari ya kayar da shi

Abuja - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sai da yayi takarar kujerar gwamna sau hudu kafin ya samu nasara daga karshe a shekarar 1999.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin ganawa da shugabannin kungiyoyin magoya bayansa a birnin tarayya Abuja, rahoton Daily Nigerian.

Atiku yace yayi farin ciki matuka ganin matasa sun musharaka cikin siyasar kasa saboda babbar manufarsa itace horar da matasa don mika musu mulki.

Kara karanta wannan

Jerin rukunin mutane 4 da ke takaicin bayyanar burin Osinbajo na gaje Buhari

Atiku Abubakar
Sai da nemi kujerar gwamna sau 4 kafin na yi nasara a 1999, Atiku Abubakar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Ina farin cikin ganin matasa da yawa suna zuwa wajena suna ayyana niyyar takara kujerun siyasa, wasu yan majalisar jiha, wasu majalisar dokokin taraya, wasu gwamna gwamna ma suke so."
"Nima haka na fara. Na fara ina dan shekara 30. Lokacinmu yaki mukayi da mulkin Soja."
"A siyasa, kana bukakar mayar da hankali, jajircewa da zama mai manufa. Misali, na yi takarar gwamna sau hudu kafin aka zabeni daga karshe. Haka siyasa take."

1992, 2007, 2011, 2015 da 2019: Tarihin takarar Shugaban kasa 6 da Atiku Abubakar ya yi

Mun tattaro lokutan da Atiku Abubakar ya nemi kujerar shugaban kasar Najeriya a babban zabe ko zaben fitar da gwani, ko akalla ya yi niyyar neman mulki.

Atiku Abubakar ya fara tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar SDP a zaben 1999 bayan an haramtawa su Janar Shehu Musa ‘Yar’adua shiga siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel