Sunayen gwamnonin da suka gana da Tinubu a Abuja bayan bayyanar burin Osinbajo

Sunayen gwamnonin da suka gana da Tinubu a Abuja bayan bayyanar burin Osinbajo

FCT, Abuja - Jim kadan bayan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana burinsa na zama shugaban kasa a ranar Litinin, 11 ga watan Afirilu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da wasu gwamnonin da aka zaba na APC.

Kafin bayyanar burin Osinbajo a ranar Litinin, ya karba bakuncin wasu gwamnonin APC a gidansa da ke fadar shugaban kasa domin buda baki a ranar Lahadi, 10 ga watan Afirilu.

Sunayen gwamnonin da suka gana da Tinubu a Abuja bayan bayyanar burin Osinbajo
Sunayen gwamnonin da suka gana da Tinubu a Abuja bayan bayyanar burin Osinbajo. Hoto daga @Mr_JAGS
Asali: Twitter

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, gwamnoni 12 na APC ne suka halarci taron da Tinubu ya shirya inda 10 suka halarci na Osinbajo.

A watannin baya, Tinubu ya bayyana burinsa inda ya bude wa sauran 'yan siyasa hanya na bayyana burinsu na shugabancin kasa a wata tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani da Hotuna: Tinubu ya sa labule da gwamnonin APC jim kaɗan bayan Osinbajo ya shiga takarar 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakan na nuna cewa zai yi takara da Osinbajo da wasu jiga-jigan APC a zaben fidda gwani.

Abinda Tinubu ya sanar mana yayin da muka zanta da shi bayan bayyanar burin Osinbajo

Ga jerin sunayen gwamnonin da suka halarci ganawa da Tinubu:

1. Nadir El-Rufai na jihar Kaduna

2. Dapo Abiodun na jihar Ogun

3. Simon Lalong na jihar Filato

4. Abdullahi Ganduje na jihar Kano

5. Atiku Bagudu na jihar Kebbi

6. Mai Mala Buni na jihar Yobe

7. Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas

8. Hope Uzodinma na jihar Imo

9. Abdullahi Sule na jihar Nasarawa

10. Muhammad Badaru na jihar Jigawa

11. Gboyega Oyetola na jihar Osun

12. AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara

Abinda Tinubu ya sanar da mu, Gwamnonin APC

A yayin bayani bayan taron, Gwamna Bagudu na jihar Kebbi wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC, ya ce Tinubu ya sanar da gwamnonin niyyarsa ta neman kujerar shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar Osun

A kalamansa: "Da safiyar nan, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gana da wasu daga cikin gwamnonin APC inda ya sanar da abinda ya bayyana na neman ofishin shugaban kasa nan da 2023. Ya bayyana mana dalilansa, tunaninsa da kuma sakonsa."

Osinbajo ba ɗa na bane, Tinubu ya maida martani ga Mataimakin shugaban ƙasa

A wani labari na daban, jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ba ɗan sa bane ba.

Tinubu ya yi wannan furucin ne a Abuja yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan gana wa da gwamnonin APC 12, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Taron wanda ya gudana a gidan gwamnan Kebbi dake Asokoro, a birnin Abuja, ya zo ne awanni bayan mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ayyana shiga tseren gaje Buhari a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng