Ramadan: Wasu muhimman Lokuta 5 masu Albarka da ya kamata Musulmi ya Amfana da su

Ramadan: Wasu muhimman Lokuta 5 masu Albarka da ya kamata Musulmi ya Amfana da su

  • Al'ummar Musulmai a faɗin Duniya sun kammala Goman farko ta Ramadana kuma tuni suka shiga Goma ta biyu
  • Yayin da Musulmai suka jajirce wajen ayyukan Ibada da kai kukansu gaban Allah, mun tattaro muku wasu lokuta 5 masu muhimmanci
  • Watan Ramadan shi ne wata na Tara a jerin watannin Kalandar Musulunci, kuma wata mai daraja da falala

A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah, yanzun al'ummar Musumai na duniya sun kammala kashin 10 ta farko na azumin watan Ramadan, sun shiga ta biyu.

Kasancewar sun san daraja da Albarkan watan, da yawan Musulmai sun ƙara jajircewa wajen samun rabo da gamdakatar a Watan.

Aminiya Hausa ta tattaro muku wasu lokuta biyar masu matuƙar muhimmanci da ya kamata kowane Musulmi ya tuna da su kuma ya ribace su.

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Adalcin Shaikhul Islam Ibn Taimiyya (RH), Sheikh Dr Sani Rijiyar Lemo

Addu'a lokacin watan Azumin Ramadan.
Ramadan: Wasu muhimman Lokuta 5 masu Albarka da ya kamata Musulmi ya Amfana da su Hoto: pinterest.com
Asali: UGC

1. Lokacin yin sahur

Lokacin Sahur wani lokaci ne mai tattare da Abarka kuma Musulmai kan yi Sahur a ƙarshen ƙashi na uku na dare kafin fitowar Alfijir.

Sulusin dare na ƙarshe a Musulunci yana daga cikin irin lokutan da Allah ke amsar addu'ar bayinsa.

An ruwaito Manzon Allah (SAW) ya na cewa a kashin ƙarshe na dare, Allah ya na saukowa zuwa Sama ta ɗaya, irin wacce ta dace da shi, ya ce:

"Ina mai rokon gafara daga wurina in gafarta masa, ina mai rokon wani abu a wurina, na biya mishi bukatunsa."

2. Alfijir da La'asar

Lokacin fitowar Alfijir da kuma na La'asar lokuta ne masu muhimmanci, wanda Mala'ikun da ke rubutu ayyukan bawa suke canza aiki.

A kowace rana da yamma Mala'iku da ke rubuta ayyukan bayi daga Alfijir zuwa yamma zasu miƙa aiki ga mala'ikun da zasu cigaba daga yamma zuwa Alfijir.

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Azumi Cikin Tsananin Zafi, Tare da Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Duk da Allah (SWA) ya san duk abinda ke faruwa kuma shi ne cikakken masani, idan Mala'iku suka koma sai ya tambaye su me suka baro bayinsa na aikata wa?

Bisa wannan, domin samun shaida mai kyau daga bakin Mala'iku masu tsarki kuma a gaban Allah, abu ne mai kyau mu maida hankali wajen yin ayyuka nagari da Ambaton Allah.

3. Bayan Sallar kowace Farilla

Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya zauna ya cigaba da Ambaton Allah bayan ya kammala sallar Farilla to Mala'iku zasu cigaba da roƙa mishi gafara da rahama a wurin Allah

4. Bayan Sallar Asuba zuwa fitowar rana

Wannan lokaci ne mai Albarka, Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya zauna bayan kammala Asuba ya cigaba da Zikiri har rana ta riske shi, kuma ya tashi ya yi Sallah Raka'a biyu, za'a rubuta mishi Ladan aikin hajji cikakke.

5. Bayan Ladan ya gama kiran Sallah

Kara karanta wannan

Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Ja Hankali

Dai-dai lokacin da ladan ya gama kiran Sallah wani muhimmin lokaci ne da Musulmi zai iya samun ceton Manzon Allah (SAW) idan ya ribace shi.

Ya tabbata a cikin hadisi daga Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya amsa kiran Sallah, bayan gama wa ya biyo da Addu'a kamar haka;

"Allaahumma Rabba haathihid-da 'watit-taammati wassalaatil-qaa'imati, 'aati Muhammadanil-waseelata walfadheelata, wab 'ath-hu maqaamam-mahmoodanil-lathee wa'adtahu, 'innaka laa tukhliful-mee'aad."

Wanda ya yi wannan zai samu ceton Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, Allah ya sa mu dace.

A wani labarin kuma Abubuwan da ya kamata kusani masu muhimmanci game da watan Azumin Ramadan

Azumtar watan Ramadana na ɗaya daga cikin abubuwa 5 da aka gina Musulunci a kan su kuma shi ne wata na Tara.

Kowane Musulmi an umarce shi ya Azumci watan na kwana 29 ko 30, amma akwai wasu rukunin mutane da Allah ya musu rangwame.

Kara karanta wannan

Ramadana: Yin azumi na karawa mutum karfi da lafiyar jiki – In ji kwararriyar likita

Asali: Legit.ng

Online view pixel