Ramadaniyyat 1443: Adalcin Shaikhul Islam Ibn Taimiyya (RH), Sheikh Dr Sani Rijiyar Lemo

Ramadaniyyat 1443: Adalcin Shaikhul Islam Ibn Taimiyya (RH), Sheikh Dr Sani Rijiyar Lemo

Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo malami ne a tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar Bayero da Kano kuma shugaban cibiyar nazarin addinai a jami'ar.

Wannan karo, Malam ya yi magana da daya daga cikin Manyan Maluman addinin Musulunci magabata.

Adalcin Shaikhul Islam Ibn Taimiyya (RH)

1. Ҝungiyar Mu'utazilawa, ƙungiya ce ta 'yan bidi'a. Ta bayyana ƙarshe-ƙarshen daular Banu Umayya, sannan ta bunƙasa a zamanin daular Abbasiyya. Wani almajirin Al-Hasanul Basari, mai suna Wasilu ɗan Aɗa' (80-130) shi ne ya dasa dashenta na farko.

2. Ta shahara da wasu aƙidu da suka saba wa Alƙur'ani da Sunna, kamar cewa, Alƙur'ani halitta ce da kore wa Allah ƙaddara da ƙaryata ceto a ranar gobe ƙiyama da da'awar cewa wanda ya mutu yana aikata kaba'ira zai dauwama a cikin wuta, da sauransu.

Kara karanta wannan

Cikakken Bidiyo: Mataimakin shugaban ƙasa ya ayyana aniyar gaje Buhari a 2023

3. Malamai na Musulunci da dama sun yi musu martani a kan munanan aƙidunsu, daga cikinsu har da Shaikhul Islam Ibn Taimiyya a littattafansa masu yawa.

4. Amma yana daga cikin abin da Sheikhul Islam ya shahara da shi, shi ne adalci a maganganunsa tare da waɗanda yake da sabani da su, da nuna wa makaranta wuraren da suka yi abin a yaba musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ramadaniyyat 1443: Adalcin Shaikhul Islam Ibn Taimiyya (RH), Sheikh Dr Sani Rijiyar Lemo
Ramadaniyyat 1443: Adalcin Shaikhul Islam Ibn Taimiyya (RH), Sheikh Dr Sani Rijiyar Lemo
Asali: UGC

5. Cikin irin maganganunsa yana cewa:

"Babu shakka Mu'utazilawa sun fi 'yan Shi'a Rafidawa da kuma Khawarijawa alheri, domin kuwa su Mu'utazilawa sun yarda da halifancin halifofin Annabi (SAW) huɗu....Sannan suna ganin girman aikata zunubbai, sannan suna kiradadon gaskiya, kamar Khawarijawa. Ba sa ƙiƙirar ƙareraye kamar yadda Shi'a Rafidawa suke yi. Ba su yarda su yi ta-ware, su kafa garinsu daban da na sauran Musulmi ba kamar yadda Khawarijawa suke yi. Suna da littattafan Tafisirin Alƙur'ani waɗanda a cikinsu suka riƙa ba wa Manzon Allah (SAW) kariya. Suna da abubuwa kyawawa da yawa waɗanda, da su ne suka ɗara Khawarijwa da Shi'a Rafidawa.

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Abubuwan Da Suke Hana Yin ƙarya, Dr Sani Rijiyar Lemo

6. Manufarsu ita ce tabbatar da Tauhidi (Kaɗaitakar Allah) da rahamarsa da hikimarsa da gaskiyarsa da ɗa'arsa. Ginshiƙan aƙidarsu guda biyar suna ƙoƙarin tabbatar da waɗannan sifofi ne (na Allah), amma dai kuma sun tabka kurakurai a kowane ɗaya daga cikin waɗannan ginshiƙai nasu…". [Duba, Majmu'ul Fatawa, juzu'i na 13, Shafi na 97-98].

7. Dubi wannan adalci na wannan Malami Rabbani. Bai rufe idanunsa daga ganin wasu alherai nasu ba, duk kuwa da irin martani da gyararraki da ya yi ta yi musu a wurare masu yawa da suka kauce wa karantarwar Alƙu'rani da Sunna. Allah ya sa mu dace. Amin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel