Bayan kama matarsa da kwarto, dattijo ya tattara kayansa ya bar aurensu mai shekaru 30

Bayan kama matarsa da kwarto, dattijo ya tattara kayansa ya bar aurensu mai shekaru 30

  • Wani dattijo ya tattara yanasa-yanasa ya bar gidansa na aure sakamakon kama matarsa da ya yi tana cin amanar aurensu
  • Magidancin wanda ya shiga rudani ya kama uwar ‘ya’yansa hudu tana cin amanarsa da wani saurayinta ne tun tana a makarantar sakandare
  • Ya bayyana cewa a yanzu yana zaune ne a wani gida mai daki daya sannan yaransa suna kai masa ziyara ofishinsa a kullun

Wani mai amfani da shafin Twitter ya bayyana aure a matsayin damfara yayin da ya tuna yadda ya bata shekaru 30 na rayuwarsa yana zaune da matar da ya kira da “shaidaniya.”

A wani wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu, mutumin ya ce ya kama matarsa ta shekaru 30 tana cin amanarsa tare da wani saurayinta na makarantar sakandare shekaru biyu da suka shige.

Kara karanta wannan

Za mu kwamushe shi: Za a yi maganin wani dan sandan da aka ga yana busa taba a bainar jama'a

Bayan kama matarsa da kwarto, dattijo ya tattara kayansa ya bar aurensu mai shekaru 30
Bayan kama matarsa da kwarto, dattijo ya tattara kayansa ya bar aurensu mai shekaru 30 Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Mutumin ya bayyana cewa lamarin ya tursasa masa barin gidan aurensa inda ya koma zama a wani gida mai daki daya.

Matar da ake magana da kanta ta sake aurenta

Ya koka kan bacin ran da ya tsinci kansa a ciki ta sanadiyar aure sannan ya bayyana cewa matar ta je ta sake aurenta da wannan mutumin da ya kama ta suna cin amanarsa tare.

Magidancin wanda ya kasance uba ga ‘ya’ya hudu ya bayyana cewa yaran nasa suka zo gaishe shi a ofishinsa domin karbar kudin kula da dawainiyarsu a kullun.

Ya rubuta:

“Na shiga irin wannan halin, ina cikin wani hali a yanzu haka bayan aurena na shekaru 30 da yara hudu, na gano cewa matar da na ke so kuma nake ci gaba da so ta fada soyayyar wani daban. Na bar mata gidan sannan na yi hayar daki daya, yarana na zuwa ganina a kullun a ofishina domin karbar kudin abincinsu.

Kara karanta wannan

Innalillahi wa’inna illahi raji’un: Allah ya yiwa sajan Funtua wanda harin jirgin kasa ya cika da shi rasuwa

“Shekaruna biyu da barin gidana ta auri wannan mutumin da na kama su tare, ta yi ikirarin cewa suna tare da mutumin tun a zamani da take makarantar sakandare har zuwa yanzu. Hakan na nufin na yi asarar shekaru 30 na rayuwana tare da shaidaniya. Aure duk karya ce.”

Kalli wallafar a kasa:

Jama’a sun yi martani:

@wisdompro4 ya ce:

“Ka fadama kowace macen Afrika a kulla auren yarjejeniya, sai ka ga yadda za ta yi kamar yar ruwa, amma sun iya yiwa namiji wakan auren kotu har a cikin baccinsa, za su ihun auren kotu. Idan bata nan lokacin da ka yi kudinka, auren yarjejeniya ba mafita bane hatta wasu iyaye mata masu yara da ke da kudi suna bayar da shawarar hakan."

@Venorite ya ce:

“Na toshe mata fiye da hudu da na hadu da su a soyayyata ta baya. A duk lokacin da na ambaci yarjejeniya kafin aure, abu na gaba shine kana shirin saki. Mutane na sauyawa a aure. Kana iya wayar gari a gobe ka ga cewa ka auri shaidaniya sannan ka saura babu komai. Ku kulla yarjejeniyar kafin auren nan."

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

@IAmMrMeks ya ce:

“Masu cewa bayan shekaru 30 na bani dariya. Baku san mace ba duk yadda kuka kai da sani sanin juna ko na shekaru da yawa ne ko kuma kuke tare.
“Ina addu’an Allah ya baka dukka karfin da kake bukata domin fita daga wannan hali.”

Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Girgiza Yan Najeriya

A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya ta tashi daga bangaren yan mata yayin da ta shirya amarcewa da Masoyinta, wanda surar jikinsa ta nuna gajere ne.

Hotunan kafin aure na ma'auratan da Amaryan ta watsa a kafafem sada zumunta, shafin Gossipmilltv ya sake tura su a kafar sada zumunta ta Instagram.

Sanye da karamar riga iri ɗaya da wando Jeans, tsintsayen soyayyar biyu sun nuna tsantsar soyayya a Hotunansu na Kafin Aure da murmushi a fuskarsu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel