Da Dumi-Dumi: Bayan Kwashe kwanaki 56 ana yajin aiki, Gwamnatin Buhari zata gana da ASUU

Da Dumi-Dumi: Bayan Kwashe kwanaki 56 ana yajin aiki, Gwamnatin Buhari zata gana da ASUU

  • Gwamnatin tarayya ta shirya zama don cigaba da tatttauna wa da kungiyar malaman Jami'o'i ASUU yau Litinin
  • Ma'aikatar kwadugo da samar da aikin yi tace Dakta Chris Ngige ne da kansa zai jagoranci zama da wakilan ASUU
  • A yau Litinin 11 ga watan Afrilu, yajin aikin da ya tura ɗalibai gina ya shiga rana ta 56

Abuja - Gwamnatin tarayya ta hannun ministan Kwadugo da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ta shirya zama da kungiyar Malaman Jami'o'i ASUU, yau Litinin 11 ga watan Afrilu, 2022.

Punch ta rahoto cewa taron wanda aka shirya farawa da misalim ƙarfe 5:00 na yamma, zai samu halartar wakilan gwamnati da kuma na ASUU.

Shugaban ASUU da Ministan Kwadugo.
Da Dumi-Dumi: Bayan Kwashe kwanaki 56 ana yajin aiki, Gwamnatin Buhari zata gana da ASUU Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Daraktan watsa labarai da hulɗa da jama'a na ma'aikatar kwadugo ta ƙasa, Patience Onuobia, a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, ta ce Ngige ne zai jagoranci taron da kansa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tsohon hadimin shugabannin Najeriya biyu ya rigamu gidan gaskiya

Vanguard ta rahoto Sanarwan ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ministan Kwadugo da rage zaman kashe wando, Dakta Chris Ngige, zai gana da kungiyar ASUU da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin yau Litinin."

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa yajin aikin da ASUU ta tsunduma ya shiga kwana na 56 a yau Litinin, 11 ga wata.

A ranar 14 ga watan Fabrairu, 2022, ƙungiyar ASUU ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na tsawon makonni hudu biyo bayan gaza samun masalaha tsakanin kungiyar da FG game da bukatunta.

Menene manyan bukatun kungiyar ASUU?

Wasu daga cikin buƙatun ASUU sun haɗa da, sakin kuɗin gyara jami'o'i da kayan aiki, sake tattaunawa kan yarjejeniyar FGN/ASUU ta 2009, sakin kuɗin alawus na malman jami'o'i.

Wata babbar bukata da ake kai ruwa rana tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya ita ce fara amfani da UTAS wajen biyan malaman Jami'a Albashi da kuma Alawus.

Kara karanta wannan

Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Ja Hankali

Bayan ƙarewar mako hudu na farko, ASUU ta ƙara bayyana karin makonni Takwas, inda ta ce ta yi haka ne don baiwa gwamnati isasshen lokaci ta cika mata buƙatu.

A wani labarin kuma Hotunan Katafariyar Gada Mai Hawa Uku da Ganduje Ke Ginawa a Kano, Babu Irinta a Faɗin Najeriya

Gwamnatin Kano na cigaba da aikin gada mai hawa uku a Shataletalen NNPC dake Anguwar Hotoro.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce suna sa ran kammala aikin zuwa watan Satumba, an raɗa wa Gadar 'Muhammadu Buhari Interchange'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel