Ba na shakkan Tinubu ko Osinbajo, duk zan kada su - Yahaya Bello

Ba na shakkan Tinubu ko Osinbajo, duk zan kada su - Yahaya Bello

  • Gwamnan Yahaya Bello na Kogi yace shirye yake ya kara da Tinubu, Osinbajo da sauran yan takara
  • Gwamnan wanda shine mai karamin shekaru cikin wadanda suka ayyana niyyar takara yace ba ya shakkan kowa
  • Yahaya Bello yace irin namijin kokarin da yayi a jihar Kogi shi ke ban karfin gwiwan ganin zai kada su

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa ko kadan ba ya tsoron tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu ko mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a takarar kujerar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC.

Bello ya bayyana hakan a Abuja ranar Asabar yayinda taron karawa juna ilimi na yan jarida masu rahoto kan siyasa da tsaro, rahoton Punch.

Gwamnan na Kogi ya ce duk da cewa Tinubu na daga cikin iyayen jam'iyya, ko shakka babu zai iya kada shi.

Kara karanta wannan

Yadda cikin sati 2 Buhari ya magance matsalolin APC yayin da rashin tsaro ke cigaba

Yahaya Bello
Ba na shakkan Tinubu ko Osinbajo, duk zan kada su - Yahaya Bello Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A riwayar Sun, Yayinda aka tambayesa shin yana tsoron takara da manyan yan takara kujerar, Yahaya Bello yace:

"Bana tsoron kowa a takarar tikitin kujerar shugaban kasa na APC."
"Tinubu da sauran su ne suka kafa jam'iyyar, amma don ka gina tubali ba shine komai ba. Zan kayar da dukkan sauran yan takaran. Ina da komai da mai nasara ya cancanta."
"Irin namijin kokarin da nayi a jihar Kogi shi ke ban karfin gwiwa."

Yahaya Bello ya kara da cewa sama da yan Najeriya milyan 16 shirye suke su kada masa kuri'a.

Yahaya Bello: Zan Iya Sanadin Samar Da Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Mace a 2023

Yahaya Bello, gwamnan Jihar Kogi ya ce zai tsayar da mace a karon farko ta zama mataimakiyarsa in har aka tsayar da shi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a gagarumin zaben 2023 da ke karatowa, rahoton NAN.

Kara karanta wannan

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

Bello ya bayar da wannan tabbacin ne a taron GYB na biyu na shekara wanda aka shirya don harkar siyasar Najeriya da masu hada kai wurin laifuka wanda aka yi a Abuja inda ya ce matsawar aka ba shi dama zai dama tare da mata.

Gwamnan ya ce ya zage damtse wurin yi aiki tare da mata, matasa da masu nakasa kamar yadda ya yi a Jihar Kogi kuma zai tabbatar bai bar kowa a baya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel