Rahotanni masu karo da juna kan bidiyon sojoji sun kwashe 'yan ta'adda a motocinsu a Kaduna

Rahotanni masu karo da juna kan bidiyon sojoji sun kwashe 'yan ta'adda a motocinsu a Kaduna

  • Jama'a suna yada rahotanni masu karo da juna kan wasu bidiyoyi da aka ga sojoji na kwashe wadanda ake zargin 'yan bindiga ne suna zubawa a motarsu
  • Jama'a sun zargi cewa 'yan ta'addan da suka kutsa yankin Kakura ne da ke karamar hukumar Chikun wadanda sojoji da 'yan sa kai suka halaka
  • Mazauna yankin sun tabbatar da cewa sojoji da 'yan sa kai sun sheke 'yan ta'adda 16 yayin da wasu 17 suka samu miyagun raunika

Kaduna - Rudani ya bibiyi wani bidiyo da ke ta yawo wanda ke bayyana sojin Najeriya sanye da khaki suna kwashe wasu mutane da ake zargin 'yan bindiga ne zuwa motar sojoji.

Mutane da yawa sun zargi cewa 'yan bindiga ne da suka kutsa yankin Kakura da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Bayan makonni 2, iyalan fasinjoji na son tattaunawa da 'yan bindiga

Rahotanni masu karo da juna kan bidiyon sojoji sun kwashe 'yan ta'adda a motocinsu a Kaduna
Rahotanni masu karo da juna kan bidiyon sojoji sun kwashe 'yan ta'adda a motocinsu a Kaduna. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wani mazaunin Kakura ya sanar da Daily Trust cewa sojoji da 'yan sa kai sun halaka 'yan bindiga 16 a lokacin da suka kutsa yankin wurin karfe 11 na daren Asabar. Ya ce wasu 17 sun jigata bayan artabun da suka yi da jami'an tsaro.

"'Yan bindigan sun isa yankin inda suka sace mutane amma jama'ar yankin da taimakon wasu sojoji da 'yan sa kai sun yi artabu da su kuma ina tunanin an kashe 16, wasu 17 sun jigata," yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai, wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa shugaban yankin, Isiaku Madaki, ya sheka lahira a sa'o'in farko na ranar Lahadi sakamakon luguden wutan da 'yan bindigan suka yi masa har cikin gidansa da ke Kakura.

Ya ce fusatattun matasan yankin sun garzaya zuwa gidajen Fulani domin daukar fansa inda suka halaka mutum 14.

Kara karanta wannan

Ya bayyana: Adadin Mata, Maza da Yaran da yan bindigan suka sace a harin jirgin Abuja-Kaduna

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce zai nemo karin bayani kuma zai kira amma har lokacin rubuta wannan rahoton ba a ji daga wurinsa ba.

A wata takarda da Aruwan ya fitar, ya ce, "A halin yanzu babu bayani gamsasshe da za a iya samu kan wadannan bidiyoyin da ke yawo. Da zaran mun samu bayani kan aikin, za mu sanar da manema labarai da 'yan kasa."

Sai dai kamar yadda Premium Times ta ruwaito, rundunar sojin Najeriya ta yi mukusu kan bidiyon ba tare da bada karin bayani ba.

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai mugun farmaki sansanin soji, sun sheke dakaru 11

A wani labari na daban, a kalla sojoji 11 ne aka kashe a mugun hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a wani sansanin soji da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kamar yadda majiya ta shaida wa TheCable.

Kara karanta wannan

Harin jirgin Abuja-Kaduna: 'Yan ta'adda sun saki sabon bidiyon fasinjoji, suna rokon gwamnati

‘Yan bindigar da suka isa sansanin da yawansu sun kutsa cikin sansanin da ke kauyen Polwire a ranar Litinin da ta gabata inda suka yi artabu da sojojin.

Majiyar soji ta shaida wa jaridar TheCable cewa, ‘yan bindigar sun bayyana a kan babura kuma suna dauke da manyan makamai da suka hada da gurneti (RPG).

Asali: Legit.ng

Online view pixel