Bauchi: An Kama Mai Hidimar Ƙasa Na Bogi Ya Saci Wayoyi a Sansanin NYSC

Bauchi: An Kama Mai Hidimar Ƙasa Na Bogi Ya Saci Wayoyi a Sansanin NYSC

  • Rundunar ‘yan sanda Jihar Bauchi ta kama wani matashi mai shekaru 23 da ake zargin mai bautar kasar bogi ne wanda ya shiga sansaninsu da ke jihar
  • Ana zargin, Muhammed Bello Hassan ya shiga sansanin ne da ke Wailo, karamar hukumar Ganjuwa ta jihar da takardar bogin da ya gabatar
  • An kwace wayoyi biyu da sauran tsadaddun abubuwa a hannunsa wadanda ake zargin ya sace ne a sansanin, yanzu haka ana ci gaba da tuhumarsa

Bauchi - Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta kama wani Muhammed Bello Hassan mai shekaru 23 wanda ya shiga sansanin masu bautar kasa da ke Jihar Bauchi da takardun bogi, rahoton The Punch.

Ya shiga sansanin wanda ke Wailo a karamar hukumar Ganjuwa da ke jihar inda ya sace wayoyi biyu da sauran tsadaddun abubuwa kamar yadda NAN ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke magidanci da bindiga, carbin harsashi 20, shanu 31 da tumaki 28 a Bauchi

Bauchi: An Kama Mai Hidimar Ƙasa Na Bogi Ya Saci Wayoyi a Sansanin NYSC
An Kama Mai Hidimar Ƙasa Na Bogi Ya Saci Wayoyi a Sansanin NYSC a Bauchi. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan sanda sun shaida yadda Hassan ya shiga sansanin bayan mahaifiyarsa ta tambayeshi dalilin da ya hana shi kammala makaranta tare da abokansa.

Ya shiga sansanin ne don ya dauki hoto ya tura wa iyayenshi

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakili ya tabbatar da batun kamen a ranar Juma’a inda ya ce an tura musu takardar korafin an yi sata a sansanin masu hidimar kasar wacce mai gudanarwar jihar, Alhaji Namadi Abubakar ya sanya hannu a maimakon Darekta Janar din NYSC, Manjo Janar Shuaib Ibrahim.

Wakil ya ce takardar ta nuna cewa ana tuhumar wani Muhammed Bello Hassan mai lambar rijistar hidimar kasa NYSC/USS/2022/27708 da lambar jihar BA/22A/1580.

Kamar yadda ya ce:

“Mai sunan nan ya shiga sansanin masu hidimar kasar da takarda bogi. Amma daga karshe dubunsa ta cika bayan an kama shi da wayoyi biyu da sauran tsadaddun abubuwan da ya sace wa masu hidimar kasar.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

“Bayan an ci gaba da bincike har ofishin binciken sirri, kwamishinan ‘yan sanda ya bukaci jami’an binciken sirri su tuhume shi inda suka gano yadda ya shiga sansanin.”

Wakili ya bayyana cewa an gano cewa matashin ya bar wata fitacciyar jami’ar Najeriya inda ya ke karanta fannin Biology, kamar yadda Daily News 24 ta nuna.

Ya shiga sansanin ne da daddare bayan wani abokinshi ya ba shi shawarar ya shiga sansanin ya dauki hotuna sannan ya tura wa iyayensa.

Mai sayar da abinci a sansanin ya ba wayoyin

Sai dai ya saci wayoyi wadanda ya yi amfani da kudinsu wurin biyan mai abincin da ya yi siyayya wurin shi a sansanin, N17,000 inda ya mayar masa da N10,000 bayan ya bayar da wayoyin guda biyu.

Wakili ya shaida yadda aka bi wayoyin har wurin mai sayar da abincin inda ya ce mai hidimar kasar bogin da ke hannun ‘yan sanda ne ya ba shi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun bankawa Sakatariyar karamar hukuma wuta, rayuka sun salwanta

Jami’in hulda da jama’an NYSC na Jihar Bauchi, Mr Aliyu Suleiman ya sanar da NAN cewa matashin ya zo da takardar bogi da wani akwatin sata, sai dai bai yi rijista ba, ya ci gaba da boyewa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel