Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamun daukaka ne, In ji dan majalisa daga arewa
- Ibrahim Almustapha ya ce kalubalen da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu alamu ne na girma, yana mai cewa duk za su wuce su zama tarihi
- Dan majalisar mai wakiltan mazabar Wurno/Rabah na jihar Sokoto a majalisar wakilai ya kuma bukaci al'umman kasar da su hada hannu wajen magance matsalolin
- Almustapha ya kuma nuna karfin gwiwar cewa jam'iyyar APC mai mulki ce za ta sake lashe zabe a babban zaben kasar na 2023 mai zuwa
Sokoto - Dan majalisar dokokin tarayya daga jihar Sokoto, Ibrahim Almustapha, ya bayyana cewa matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu alamu ne na daukaka, cewa kasar na da ikon za ta iya tsallake su.
Almustapha wanda ke wakiltan mazabar Wurno/Rabah na jihar Sokoto a majalisar wakilai, ya bayyana hakan ne da yake zantawa da manema labarai a garin Sokoto a ranar Lahadi, Premium Times ta rahoto.
Ya ce:
“A ganina, ina kallon yawancin wadannan matsaloli, musamman matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta a matsayin alamar daukaka, kasashe da dama da suka daukaka sun fuskanci matsaloli masu tarin yawa a hanyarsu na kaiwa inda suke.
“Na yarda irin hakan ne zai kasance ga Najeriya kuma da zaran mun shawo kansu, Najeriya za ta daukaka a kowani bangare na ayyukan dan adam, ta fuskacin tattalin arziki, ababen more rayuwa, wutar lantarki da sauransu.
“Abun da muke bukata shine hada kai a matsayin kasa da gaskiya, wajen magance matsalolin. Ya kamata yan Najeriya da ke da dabi’ar murna idan abun bakin ciki ya faru su daina.
“Masu kai bayanai da kayayyaki ga yan bindiga da yan fashi da makami su daina sannan wadanda aka daurawa alhakin yaki dasu su zamo masu gaskiya.”
Mista Almustapha ya ce koda dai Najeriya ta cimma wasu nasarori a yaki da yan ta’addan Boko Haram a arewa maso gabas, akwai bukatar kara jajircewa.
Ya kara da cewa:
“Ina ganin yankin arewa maso gabas ya samu zaman lafiya na dan lokaci yanzu, a zahirin gaskiya lamarin ya sauya daga yadda yake a 2015 lokacin da jam’iyyar APC ta hau mulki.”
Ya nuna yakinin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta cimma nasara a kokarinta na magance matsalolin rashin tsaro da ya addabi kasar.
Dan siyasar ya bayyana cewa sabon shugabancin APC zai gyara jam’iyyar gabannin babban zaben 2023. Ya kuma ce jam’iyyar mai mulki za ta lashe zaben 2023 ba tare da wani kalubale ba, rahoton The Nation.
Abun da ya sa yaki da yan fashi ke da matukar wahala – Gwamnatin Buhari
A gefe guda, Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa abu ne mai wahala a yaki yan fashin daji saboda yanayin da suke kai farmaki.
Daily Trust ta rahoto cewa ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a shirin gidan radiyo na Bond FM a karshen mako.
Ya ce gwamnati mai ci ta zuba jari sosai wajen magance matsalar rashin tsaro, inda ya kara da cewa kokarin zai fi yin tasiri ne idan al’umman kasar suka marawa kokarin da gwamnati ke yi baya.
Asali: Legit.ng