Wutar lantarkin kasa ta sake lalacewa, Legas, Abuja Kaduna da wasu jihohi na cikin duhu

Wutar lantarkin kasa ta sake lalacewa, Legas, Abuja Kaduna da wasu jihohi na cikin duhu

  • Karo na uku cikin wata guda, tushen wutar lantarki Najeriya ya sake lalacewa gaba daya
  • Gwamnatin taayya ta bayyana cewa yanzu haka tana bincike kan abinda ya haddaa wannan lalacewa na wuta
  • Ma'aikatar wutar lantarki ta kasa ta ce barna da ake mata a hasumiyar rarrabe wutar lantarki ce ke janyo lalacewar wutar kasar nan

Kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya sun bayyana dalilin da ya sa wuta ta dauke a fadin tarayya ranar Juma'a, 9 ga watan Afrilu, 2022.

Mazauna Legas, Abuja, Kano, Kaduna da sauran jihohi sun ce tun da aka dauke wuta har yanzu babu.

Akalla kamfanoni uku sun saki jawabin tabbatar da hakan a shafukan ra'ayi da sada zumuntarsu.

Sun ce tushen wutan Najeriya gaba daya ne ya lalace misalin karfe 6:30 na yammacin Juma'a.

Kamfonin da sukayi sanarwa sun hada da na Legas Eko Disco, Abuja Disco, Kano Disco da Kaduna Disco.

Kamfanin rarraba wuta na Legas, Eko Disco yace:

"Ya ku kwatamominmu, muna sanar da ku cewa wutar kasa ta lalace daga karfe 6:30 na yammacin Juma'a, 8 ga Afrilu, 2022. Abokan harkallarmu na duba yadda za'a gyara nan ba da dadewa ba."

Kamfanin rarraba wuta na Abuja AEDC yace:

"Ku sani cewa rahsin wutan da kuke fuskanta sakamakon lalacewar wuta daga matattara ta kasa ne. Wutan ya lalace misalin karfe 6:30 da 8:50 na yammacin Juma'a."

Kamfanin rarraba wutan dake baiwa Kano, Katsina da Jigawa wuta kuwa yace:

"Muna sanar da ku dalilin rashin wuta. Muna baku hakuri bisa wannan abu."

Barna a hasumiyar rarrabe wutar lantarki ce ta ka ga lalacewar wutar Ƙasa, FG

Ma'aikatar wutar lantarki ta tarayya a ranar Asabar ta ce lalacewar wutar lantarkin kasar nan ya biyo bayan barna da ake yi wa kasar a hasumiyar rarrabe wutar lantarkinta.

Jawbain yace:

"Karin bayani kan takarda da muka saki ga manema labarai, muna son sanar da jama'a cewa dalilin rashin wutan nan shi ne ayyukan mabarnata masu barna a hasumiyar rarrabe wutar lantarki da ke Odukpani Ikot Ekpene wanda yasa aka rasa 400MW na wutar da ake samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel