Abun da ya sa yaki da yan fashi ke da matukar wahala – Gwamnatin Buhari

Abun da ya sa yaki da yan fashi ke da matukar wahala – Gwamnatin Buhari

  • Ministan labarai, Lai Mohammed ya bayyana cewa yanayin da yan fashin daji ke kaddamar da hare-harensu ya taimaka wajen kawo cikas a yaki da ta’addanci
  • Mohammed ya ce ba zai yiwu a tayar da yan fashin daji gaba daya ta hanyar dana masu bam ba saboda bayin Allah da ke zaune a kewaye da su
  • Ya yi kira ga yan kasar da su taimakawa gwamnati a yaki da take da matsalar rashin tsaro domin ta haka ne kawai za a cimma nasara

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa abu ne mai wahala a yaki yan fashin daji saboda yanayin da suke kai farmaki.

Daily Trust ta rahoto cewa ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a shirin gidan radiyo na Bond FM a karshen mako.

Kara karanta wannan

Ya taro 'Match': Bidiyon tashin hankali yayin da mai tura kuran ruwa ya kwarzane mota Benz

Abun da ya sa yaki da yan fashi ke da matukar wahala – Gwamnatin Buhari
Abun da ya sa yaki da yan fashi ke da matukar wahala – Gwamnatin Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Ya ce gwamnati mai ci ta zuba jari sosai wajen magance matsalar rashin tsaro, inda ya kara da cewa kokarin zai fi yin tasiri ne idan al’umman kasar suka marawa kokarin da gwamnati ke yi baya.

Da yake martani ga shawarar Gwamna Nasir El-Rufai na yin hayar sojoji daga waje, Mohammed ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gwamna El-Rufai ya yi magana ne saboda damuwa da halin da ake ciki. Watakila ya yi magana ne saboda yanayin yadda yan fashin suka jajirce wajen kai hare-hare.
“Ba za a iya kwatanta sojojin haya da rundunonin tsaronmu ba; yaki da yan fashi yana da matukar wahala ne saboda yanayin. Ba za mu iya zuwa da karfi don tayar da su da bam ba idan ba haka ba za a kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba wadanda ke zama a kewaye da su, kuma bama so hakan ya faru.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

“Idan muka kwaso sojojin haya domin su yaki yan fashi, sai mu saka a zukatanmu cewa su yan haya ne kawai ba wai jami’an tsaronmu ba wadanda za su koma koina bayan kammala aikinsu.”

A rahoton Thisday, ministan ya kuma roki yan Najeriya da su hada hannu a yaki da yan fashin, cewa gwamnatin tarayya ba za ta iya yi ita kadai ba.

“Muna kuma rokon yan Najeriya da su hada hannu a wannan yakin saboda suna da rawar ganin da za su taka a wajen magance wannan matsala ta rashin tsaro. Hakan ya kasance ne saboda wadannan miyagun da ake kira yan fashi suna zama ne a tsakaninmu; suna kuma hulda da mutane.
“Su wa ke kai masu abinci? Bugu da kari, suma suna da ubannin gidan da suke haya. Ya kamata mutane su dunga fallasa wadannan miyagu sannan ne za mu fara ganin sakamakon kokarin da gwamnati ke yi.

Kara karanta wannan

Sun Gane Shayi Ruwa Ne: 'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

“Muna ta iya bakin kokarinmu a yaki da yan fashi ta hanyar cika tsarin tsaronmu da kayan aiki. Gwamnati ta siya jiragen yaki domin su yi yaki tare da sojoji. Ba mu yi kasa a gwiwa ba.
“An kuma baiwa ‘yan sanda kulawar da ta dace, kuma a kwanan baya, wannan gwamnati ta dauki ‘yan sanda 25,000 aiki tare da tura su jihohinsu. Wannan zai taimaka sosai wajen tsaron al’umma.
"Akwai ayyuka da dama da ke ci gaba da yi a fannin samar da tsaro.”

Borno: Dubun ƴan ta'adda ta cika, soji sun ragargajesu tare da ceto mata da ƙananan yara

A wani labarin, 'Yan ta'adda sun gamu da gamonsu a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno yayin da dakarun sojin Najeriya suka ceto mata 43, kananan yara da wani tsoho.

Dakarun sojin Najeriya na bataliya ta 202 sun lallasa 'yan ta'addan Boko Haram yayin da suka je kakkabar daji a yankin arewa gabas na jihar Borno, PR Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Korarren Limamin Abuja ya magantu, ya sanar da sabon mukamin da ya samu

Birged ta 21 dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno ta na karkashin kulawar Birgediya Janar Waidi Shayibu, wanda shi ne babban hafsan soja mai bai wa Div 7 umarni na rundunar sojin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel