Kwanaki bayan korar Sheikh Khalid daga limanci, masallata sun ragu, an tsananta tsaron masallacin
- Kwanaki bayan da kwamitin masallacin Apo ya dakatar da Sheikh Nuru Khalid, an gano cwa masallata sun ragu a masallacin
- A Jum'ar da ta gabata, an tsananta tsaro inda 'yan sanda da jami'an DSS suka dinga zare ido tare da bincikar ababen hawa
- Wani jami'in tsaro masallacin da ya bukaci a boye sunansa, ya ce kowa ya sha matukar mamakin korar Sheikh Khalid da aka yi
FCt, Abuja - Bayan mako daya da korar Sheikh Nuru Khalid a matsayin babban limamin masallacin 'yan majalisu na kwatas din Apo da ke Abuja, an cigaba a sallar Juma'a a masallacin amma an lura da cewa masallata sun ragu a Juma'ar da ta gabata ba kamar yadda aka saba ba.
Har ila yau, an tsananta tsaro a yayin da motoci ke shige da fice a farfajiyar masallacin inda jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da jami'an farin kaya ke bincikarsu, Politics Digest ta tabbatar.
Sheikh Khalid, wanda aka fi sani da Digital Imam, an dakatar da shi kuma daga bisani aka kore shi daga limancin masallacin bayan kwamitin kula da masallacin ya zargesa da yin hudubar caccakar Buhari kan yadda ya yi wa tsaron kasar nan rikon sakainar kashi.
Politics Digest ta yi sallar Juma'a a masallacin kuma ta lura cewa komai shiru sannan babu hayaniya a ciki da wajen masallacin.
Wani jami'in tsaron masallacin wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce korar Sheikh Khalid ya matukar basu mamaki.
Ya ce: "Kamar dai yadda kuka gani, mutane da yawa ba su zo sallah ba yau. Wurin nan ya saba zama a cike amma yau labarin ya sauya. Amma a hankali jama'a za su dawo tare da cigaba da sallah a masallacin."
A dayan bangaren, Limamin da ya jagoranci sallar Juma'an, Sheikh Abdullahi Adamu Funtua, ya ki zantawa da manema labarai a yayin da suka tunkaresa.
Hadimar Buhari ta sanar da hakikanin dalilin korar Sheikh Nuru Khalid daga limanci
A wani labari na daban, hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Lauretta Onochie, ta yi magana kan korarren limamin masallacin Apo da ke Abuja, Sheikh Khalid, wanda aka kora bayan wata huduba da ta janyo cece-kuce a cikin kwanakin nan.
Ta wallafar a shafinta na Twitter a ranar Litinin, 3 ga Afrilu inda ta gabatar da nau'ikan rahotan guda biyu kan makomar malamin addinin Islama da kuma abin da ya kai ga korar shi daga limanci.
Da farko ta musanta labarin da ake yadawa inda aka ce an dakatar da Sheikh Khalid ne saboda sukar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin tsaro.
Asali: Legit.ng