Korarren Liman Nuru Khalid: A da mimbarin masallacin Apo ne cibiyar kamfen din Buhari

Korarren Liman Nuru Khalid: A da mimbarin masallacin Apo ne cibiyar kamfen din Buhari

  • Korarren limamin masallacin rukunin gidajen 'yan majalisu ya sake tofa albarkacin bakinsa game da mulkin Buhari
  • Ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin, inda yace bai taba danasanin abin da ya aikata ba
  • Ya kuma bayyana cewa, a da masallacin da aka kore shi nan ne cibiyar yiwa Buhari kamfen don neman kuri'u

Abuja - Korarren babban limamin masallacin rukunin gidan 'yan majalisu da ke a Abuja kuma wanda ya kafa gidauniyar bincike da da'awar muslunci, Sheikh Nuhu Khalid, ya bayyana cewa a da “mimbarin masallacin Apo ya taba zama cibiyar kamfen din Buhari.”

Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da ya fito a shirin Daily Politics, wani shiri a gidan talabijin na Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dole malamai su dunga fadar gaskiya kan halin da Najeriya ke ciki – Sheikh Khalid

Sheikhu Nuru Khalid, korarren liman a Abuja
Korarren Liman Nuru Khalid: A da mimbarin masallacin Apo ne cibiyar kamfen din Buhari | Hoto: newsdigest.ng
Asali: UGC

An dakatar da Sheikh Khalid ne a masallacin na Apo bayan wani wa'azinsa na sukar gwamnati ya yi ta yaduwa, sakamakon haka yasa aka kore shi daga mukaminsa saboda ya yi tsokaci kan dakatar da shi.

Biyo bayan harin bam din da wasu ‘yan ta’adda suka kai kan jirgin kasan fasinja a hanyar Kaduna, wanda ya yi sanadin kashe wasu fasinjoji tare da yin awon gaba da wasu da dama, malamin ya zargi gwamnati da sakaci da halin ko in kula.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamitin masallacin daga nan ya dakatar da shi, daga baya kuma ya kore shi baki daya, lamarin dama tsakaninsa da shugaban kwamitin masallacin ne Sanata Dan Sadau.

Limamin ya ce gara ya mutu da yunwa da ya zama limamin da ba zai iya fadin gaskiya ba, musamman a wannan lokaci da rayuwa ke kara tabarbarewa da zama abin tsoro a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sama bai rikito ba a lokacin da na caccaki Jonathan, inji Sheikh Nuru Khalid

Babu abin da zan rasa, ina nan kan maganata

Jaridar Daily Trust ta tattaro Sheikh Khalid na cewa:

“Ba ni da abin da zan rasa. Game da wannan, ina nan daram kan maganata. Na gwammace in mutu da yunwa da na yi shuru ana kashe mutane. Ana kai wa jiragen kasa hari tare da toshe hanyoyi kuma (akwai) zubar da jini a ko'ina.
“Ina zaune a wani yanki. Yarana suna zuwa makarantun gwamnati kuma ina hulda da mutanen yankin. Don haka na san halin da al’ummar kasar nan ke ciki.”

Limamin ya ce har sau uku wasu mutane a cikin gwamnati suna kokarin rufe bakinsa daga martani da sharhi kan nakasun wannan gwamnati, amma ya ki sauraransu.

Ya kara da cewa:

“Idan gwamnati ba ta ji dadi ba, to muna tambaya wanene shugaban kasa kuma wa ke shan wahala? Ashe ba su ne mafi rinjaye ba. Talakawa sun fi muhimmanci shi ya sa muke kiran ma’aikatan gwamnati ma’aikatan al'umma. Dole ne a kiyaye rayukan talakawa.”

Kara karanta wannan

Korarren Limamin Abuja ya magantu, ya sanar da sabon mukamin da ya samu

Wadanda suka kai hari jirgin Abuja-Kaduna sun saki bidiyo, sun ce ba kudi suke bukata ba

A wani labarin, 'yan ta'addan da suka kai hari jirgin kasan Abuja-Kaduna sama da mako daya sun saki bidiyonsu na farko tun bayan harin da yayi sanadiyar halakar mutum akalla takwas.

A sabon bidiyon da suka saki ranar Laraba, sun bayyana cewa ba kudi suke bukata ba, gwamnati ta san abinda suke bukata.

Sun haska bidiyon ne tare da Shugaban bankin noma, Alwan Hassan, inda suka ce zasu sake shi albarkacin tsufarsa da watar Ramadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.