Bauchi: 'Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Da Bindigu, Shanu Da Tumaki 59 Da Kare
- Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta samu nasarar kama wani mutum mai shekaru 40, Ahmadu Shuaibu, da bindiga kirar AK-47 da sauran makamai
- Har ila yau, an kama mutumin, wanda mazaunin Bakin Ruwaji ne da ke karamar hukumar Toro da shanu 31, tumaki 28 da kare daya
- Kakakin rundunar ‘yan sandan, Ahmed Wakil, ya bayyana hakan a wata takarda wacce ya saki a ranar Laraba
Bauchi - Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta kama wani Ahmadu Shuaibu mai shekaru 40 da bindiga kirar AK-47 da sauran miyagun makamai tare da shanu 31, tumaki 28 da kare guda daya
‘Yan sanda sun kama Shuaibu, mazaunin Bakin Ruwaji da ke karamar hukumar Toro a Jihar Bauchi yayin da suka fita sintiri, The Punch ta ruwaito.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Ahmed Wakil, ya bayyana hakan a wata takarda wacce ya saki a ranar Laraba.
Ya bayyana inda ya siya makaman
A takardar kamar yadda jaridar Today ta nuna, SP Wakil ya bayyana cewa:
“A ranar 15 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 8 na safe, rundunar ‘yan sanda ta fita sintiri Nabordo da ke karamar hukumar Toro inda ta ci karo da Ahmadu Shuaibu mai shekaru 40 a Bakin Ruwaji a karamar hukumar Toro.
“Bayan bincike shi ne aka kama shi da bindiga kirar AK-47 da sauran miyagun makamai, shanu 31, tumaki 28 da kare daya.
“Yayin da aka tuhume shi ne ya tabbatar da cewa ya siya makaman ne daga hannun wani Ibrahim a Jihar Taraba. Bayan kammala bincike za a tura shi kotu.”
‘Yan sandan sun kwace kayan shaye-shaye a hannun wasu ‘yan daba
Har ila yau, kakakin ya shaida yadda rundunar ‘yan sanda ta kama mutane 21 wadanda duk ‘Yan Sara Suka ne, kungiyar da ta addabi mazauna jihar.
Ya ce an kama su ne da misalin karfe 9:15 na dare a ranar 4 ga watan Afirilun 2022 a Unguwar Hardo da Unguwar Mahaukata da ke yankin.
Wakil ya ce an kwace kayan shaye-shaye daga hannun ‘yan daban tare da wata waya kirar Tecno, adduna 4 da wukake 2.
'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci
A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.
A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.
Kamar yadda takardar tazo:
“An yi kamen ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri akan yadda ake yawan ganin wani mai kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.”
Asali: Legit.ng