Kano: Bene ya rushe, ya halaka rayuka 2, wasu 3 sun matukar jigata a Hotoro

Kano: Bene ya rushe, ya halaka rayuka 2, wasu 3 sun matukar jigata a Hotoro

  • An yi rashin rayukan mutane 2 yayin da wasu uku suka samu raunika masu firgitarwa a rushewar wani bene mai hawa daya a Kano
  • An gano cewa, lamarin ya faru ne wurin karfe 3 da minti 8 na daren Asabar yayin da matasan ke kwance a kangon ginin da ke kwatas din Hotoro
  • Wannan ne karo na biyu da gini ke rushewa cikin wata 1 inda wani bene mai hawa 3 ya murkushe mutane a titin Ahmadu Bello da ke Kano

Kano - Mutum biyu sun rasa rayukansu inda wasu ukun suka samu miyagun raunika masu barazana ga rayuwarsu bayan wani bene hawa daya da ake ginawa ya rushe a kwatas din Hotoro da ke Kano.

Mamatan biyu masu suna Aliyu Sulaiman mai shekaru 27 da Abdulganiyyu Sulaiman duk almajiran wata makaranta ne da ke kusa, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke magidanci da bindiga, carbin harsashi 20, shanu 31 da tumaki 28 a Bauchi

Malaminsu ya sanar da Premium Times cewa, lamarin ya auku ne wurin karfe 3 na daren Asabar yayin da mamatan ke bacci a cikin kangon.

Kano: Bene ya rushe, ya halaka rayuka 2, wasu 3 sun matukar jigata a Hotoro
Kano: Bene ya rushe, ya halaka rayuka 2, wasu 3 sun matukar jigata a Hotoro. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Duk kokarin samun kakakin hukumar kwana-kwana na jihar Kano ya gagara. Wannan ne karo na biyu da gini ke rushewa a jihar a cikin wata 1.

A ranar 17 ga watan Maris, hukumar kwana-kwana ta jihar ta sanar da mutuwar rai daya tare da jigatar wasu mutane masu yawa bayan wani gini mai hawa uku ya rushe a kan titin Ahmadu Bello da ke jihar Kano.

An tattaro cewa, benen wanda ake ginawa ya fadi yayin da wasu ma'aikata masu yawa ke cikinsa.

Hukumar kashe gobara ta jihar daga bisani sai ta bayyana cewa, ma'aikata biyu kacal ne suke cikin ginin yayin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi

Takardar da suka saki ta bayyana cewa, yayin da aka ceto mutum daya da ransa, dayan an same shi baya gane wanda ke kansa inda daga bisani yace ga garinku.

'Yan sandan Kano sun bindige masu satar mutane 3, sun ceto wasu mutane

A wani labari na daban, jami’an ‘yan sanda a Kano sun yi nasarar bindige wasu masu garkuwa da mutane a kalla uku tare da ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a hannunsu, Vanguard ta ruwaito.

Kakakin rundunar ‘yan sandanjihar, SP Abdullahi Haruna wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Kano a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce an kashe masu garkuwar ne a wani artabu da ya barke tsakanin masu garkuwa da mutanen da jami'an tsaro.

Vanguard ta ruwaito cewa, SP Haruna ya ce an kubutar da wadanda aka sace ba tare da jin rauni ba, kuma tuni aka mika su ga iyalansu.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel