Da dumi-dumi: ‘Yan ta’adda sun kai farmaki a jihar Neja, sun sace mutane da dama
1 - tsawon mintuna
Wani rahoton da jaridar Punch ya fitar ya ce, wasu 'yan ta'adda sun yi garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba a jihar Neja.
Rahoton ya tattaro cewa, an ce ‘yan ta’addan sun kai farmaki a unguwar Daza da ke karamar hukumar Munya ta jihar, inda suka yi ta harbe-harbe ba kakkautawa.
![Yadda 'yan ta'adda suka farmaki jihar Neja Yadda 'yan ta'adda suka farmaki jihar Neja](https://cdn.legit.ng/images/1120/051fa9efb84e17a8.jpeg?v=1)
Asali: UGC
Mazauna garin da dama sun tsere daga yankin sakamakon harin da aka kai a daren jiya Alhamis.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng