Dangote ya hada N380bn a cikin wata 3, ya zarce hamshakan attajiran Rasha 4

Dangote ya hada N380bn a cikin wata 3, ya zarce hamshakan attajiran Rasha 4

  • Tun daga watan Fabrairu, duniya ta shiga gunaguni game da mamayar Rasha a kasar Ukraine, lamarin da ya jefa miliyoyin 'yan Ukraine cikin mawuyacin hali
  • Sai dai bisa ga dukkan alamu ba 'yan kasar Ukraine ne kadai ke kage ba, domin kuwa hudu daga cikin attajiran Rasha sun rasa mukaminsu a jerin attajirai, Aliko Dangote ya haura
  • Dangote, wanda a farkon 2022 ke cikin mutane 100 mafi arziki da ke raye a duniya, ya tsallake matsayi 21 kuma a yanzu ya zama na 79 a duniya

Attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika, Aliko Dangote, yanzu ya fi kusan dukkan attajiran kasar Rasha, banda hudu daga cikinsu.

A cewar jadawalin Bloomberg Billionaires Index, bakar fatar da ya fi kowa kudi a duniya a yanzu yana da kimanin dala biliyan 20 bayan da ya samu sama da dala miliyan 915 (N380.38bn) cikin watanni uku kacal.

Kara karanta wannan

An sake samun matsala, an rasa rai yayin da wani jirgin kasa ya samu hadari a Kaduna

Kudin Dangote sun karu
Dangote ya samu sama da N380bn a cikin wata 3, ya zarce hamshakan attajiran Rasha 4 | Hoto: nairametrics.com
Asali: Getty Images

Sabon kari na arzikin da ya samu na nuni da cewa Aliko Dangote ya zama attajiri na 79 a raye a duniya.

Shigar Dangote 2022

Dangote dai bai shiga 2022 da kafar dama, domin kuwa ya yi asarar dala miliyan 244 a rana guda bayan kare 2021 a wani matsayi mai inganci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dan kasuwan ya fado zuwa na 100 a jerin masu kudin duniya, inda ya mallaki dala biliyan 19.1 kacal.

Sai dai kuma labarin ya sauya sosai bayan ‘yan makonni kadan, kamar yadda a karshen watan Janairun 2022 ya nuna, Dangote ya hau matsayi na 91 a jerin attajiran duniya da zunzurutun kud akalla dala biliyan 19.5.

Haka dai ya ci gaba da habaka a Fabrairu 2022 kuma ya kare watan da zunzurutun dukiyar da ta kai dala biliyan 20.0 yayin da kuma ya yi tsalle ya zuwa matsayi na 84.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ga 'yan Najeriya: Ku tarawa 'yan uwanku talakawa da harin jirgi ya shafa kudin magani

A baya-bayan nan a cikin Maris ya hau daya daga cikin mafi girman matakin da ya taba kasancewa.

Rushewar arzikin attajiran Rasha ya taimaka wa habakar Dangote

Faduwar hamshakan attajiran kasar Rasha ne ya kuma taimaka wa Dangote wajen samun nasarar tsallaka matakai a jerin attajiran duniya.

Lokacin da aka shiga 2022, akwai wasu hamshakan attajiran Rasha bakwai da suka dara Dangote arziki.

Sun hada da:

  1. Leonid Mikelson
  2. Vladimir Potanin
  3. Alexei Mordashov
  4. Vladimir Lisin
  5. Vagit Alekperov
  6. Gennady Timchenko
  7. Alisher Usmanov

Ya zuwa karshen Maris 2022, Dangote yanzu ya fi dukkan hamshakan attajiran na kasar Rasha arziki idan aka cire Vladimir Potanin, Leonid Mikhelson, Alexey Mordashov da Vladimir Lisin.

Kudin Dangote sun kara yawa da N1.5bn yayin da aka kaddamar da kamfanin takinsa

A wani labarin, a yau Talata 22 ga watan Maris ta kasance ranar farin ciki ga attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka; Aliko Dangote.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Jami'an Kwastam Sun Kama 'Ɗan Sanda' Da Mota Maƙare Da Haramtacciyar Shinkafa a Katsina

Sa’o’i kadan bayan bude wani sabon takinsa na zamani mai iya aikin tan miliyan 3 da aka gina kan kudi dala biliyan 2.5, sabbin bayanai daga cibiyar Bloomberg sun nuna cewa dukiyar Dangote ta haura da Naira biliyan 1.5 cikin ‘yan sa’o’i kadan.

Sabon kamfanin taki na Dangote na zuwa ne a daidai lokacin da yakin kasar Ukraine ya jawo tashin gwauron zabi na iskar gas, wani muhimmin sinadarin samar da takin urea.

Asali: Legit.ng

Online view pixel