Hotunan Motoccin Alfarma Da Matawalle Ya Siya Wa Masu Sarautun Gargajiya 260 a Zamfara Ciki Har Da 'Cadillac'

Hotunan Motoccin Alfarma Da Matawalle Ya Siya Wa Masu Sarautun Gargajiya 260 a Zamfara Ciki Har Da 'Cadillac'

  • Gwamna Bello Mohammed Matawallen Jihar Zamfara ya rarraba wa shugabannin gargajiyan jiharsa motoci 260 bayan kaddamar da hedkwatocin kungiyar malamai a jihar
  • Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ne ya gabatar da rabon tare da kaddamarwar a gidan gwamnatin da ke Gusau a ranar Laraba
  • Sultan din ya yaba wa Matawalle akan dagewarsa wurin samar da walwala ga shugabannin gargajiya wanda a cewarsa hakan zai kawo hadin kan al’umma

Zamfara - Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed ya raba wa shugabannin gargajiyan jiharsa motoci 260 sannan ya kaddamar da hedkwatoci na zamani ga kungiyar malaman jihar, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Daga rabon har kaddamarwar duk Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar 111 ne ya gabatar da su a gidan gwamnati da ke Gusau a ranar Laraba, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

Hotuna: Matawalle Ya Gwangwaje Masu Sarautun Gargajiya 260 Da Motoccin Alfarma a Zamfara
Matawalle Ya Siya Wa Masu Sarautun Gargajiya 260 Da Motoccin Alfarma a Zamfara. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Hotuna: Matawalle Ya Gwangwaje Masu Sarautun Gargajiya 260 Da Motoccin Alfarma a Zamfara
Gwamnan Zamfara ya siya wa masu sarautun gargajiya motocci masu tsada. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Sarkin Musulmin ya nuna farin cikinsa kana ya mika godiyarsa ga Gwamna Matawalle akan yadda ya damu da walwalar shugabannin gargajiya, wanda a cewarsa hakan ne zai tabbatar da hadin kan al’umma.

Hotuna: Matawalle Ya Gwangwaje Masu Sarautun Gargajiya 260 Da Motoccin Alfarma a Zamfara
Hotunan motocci da Matawalle ya siya wa sarakunan Zamfara. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Matawalle ya ce ya bayar da kyautar ne don kawo hadin kai a jihar

A wata takarda wacce mai ba shi shawarwari a harkar yada labarai, Zailani Bappa ya saki, ya ce Sultan din ya yi kira ga wadanda suka samu kyautar ta musamman da su kasance masu bayar da hadin kai ga shugabancin Gwamna Matawalle ta hanyar kawo mafita don kawo karshen damuwar da ke addabar jama’a.

A bangarensa, Gwamna Matawalle ya ce ya yi hakan ne don dubar darajar shugabannin gargajiya wadanda su ne masu kulawa da harkokin addini da al’adu, kuma ba su ababen hawan zai kawo hadin kai da zaman lafiya a cikin al’umma.

Kara karanta wannan

Tsawon Shekaru 6 Ƙaramar Hukuma Ta Tana Ƙarkashin Ikon Boko Haram, Kakakin Majalisar Borno Ya Koka

Kamar yadda ya ce:

“Ganin kima da darajar da mulkina ya ke yi wa shugabanninmu na gargajiya da masarautu, mun yanke shawarar samar da sabbin motoci kirar Cadillac 2019, ga sarakai 17, 13 ga manyan dagaci sai kuma 230 ga duk wani dagacin da ke fadin jihar.”

Yanzu haka ana sauya gine-gine wasu fadojin

Gwamna Matawalle ya tabbatar musu da cewa mulkinsa zai ci gaba da aiki da shugabannin gargajiya da na addini don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Kamar yadda Nigerian Tribune ta bayyana, Matawalle ya ce:

“Ina mai tabbatar muku da cewa mulkina zai ci gaba da aiki da manufar daga daraja da kimar masarautunmu iyakar kokarinmu.
“Muna kan gyara da sauya salon gine-ginen fadajin sarakunan da ke fadin jihar nan. An kusa kammala wasu ayyukan.”

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Makarantun firamare: Gwamnan Katsina ya ba da umarnin a fara karantarwa da harshen Hausa

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya za su yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel