Cikakken Jerin Jihohin Najeriya Da Suka Fi Cin Bashi, Da Waɗanda Ke Kan Gaba Wurin Rashin Aikin Yi
Halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a yanzu yana shafar mazauna kasar da gwamnatocin jihohi a yankuna daban-daban hakan yasa suke karbo manyan bashi musamman tun shekarar 2020.
Kamar yadda aka sani, karancin samun kudaden shiga da ya shafi tattalin arzikin na da alaka da annobar COVID-19 wacce ta adabi kasashen duniya tun farkon 2019.
A cewar StatiSense, yankin kudu maso yammacin Najeriya ne kan gaba wurin karbar bashi a shekarar 2021 duba da cewa yankin ne ya karbi kashi 33 cikin 100 na bashin da jihohi 36 suka karba har da FCT a wannan shekarar.
A shekarar 2020, kudu maso kudu ne yankin da ke kan gaba wurin rashin aikin yi - inda ya ya ke kashi 25 cikin 100, kuma yankin ne ke kan gaba wurin jihohi masu yawan bashi don jihohin yankin suna cikin 10 na farko a jerin masu karbar bashin.
Ga jerin sunayen jihohin da suka fi yawan bashi a shekarar 2021 a kasa:
- Lagos
- Kaduna
- Rivers
- Ogun
- Cross River
- Imo
- Akwa Ibom
- Edo
- Bayelsa
- Delta
Ga kuma jerin jihohin da suka fi yawan mutane marasa aikin yi:
- Lagos
- Rivers
- A/Ibom
- Kaduna
- Imo
- Cross River
- Anambra
- Adamawa
- Delta, SS
- Abia
Wannan bayanan na cikin wani wallafa da hadimar Shugaban kasa, Lauretta Onochie ta yi na shafinta na Facebook.
Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.
Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.
Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.
Asali: Legit.ng