Ina goyon bayan El-Rufa'i, ya kamata mu tura yan ta'adda Lahira, Tinubu

Ina goyon bayan El-Rufa'i, ya kamata mu tura yan ta'adda Lahira, Tinubu

  • Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana goyon bayansa ga kalaman El-Rufa'i na kashe yan bindiga har maɓoyarsu
  • Jagoran jam'iyya mai mulki na ƙasa ya ce wajibi kowa ya ba da gudummuwa, a yi duk me yuwuwa wajen tsaftace kasar nan daga ta'addanci
  • Ɗan takarar shugaban ƙasan ya kuma ba da gudummuwar miliyan N50m domin taimaka wa waɗan da harin jirgi ya shafa

Kaduna - Jagoran APC na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya nuna goyon bayansa ga matsayar El-Rufa'i, wanda ya nemi a yi luguden wuta kan yan bindiga a jeji kuma a kashe su.

Tinubu ya yini a Kaduna jiya Talata domin jajantawa al'umma da kuma Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i, bisa bala'o'in da suka afka wa jihar a yan makonnin da suka shuɗe.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna El-Rufai ya fadawa Tinubu ido-da-ido a game da takarar da zai yi a 2023

Daily Trust ta rahoto Tinubu na kira da a samu haɗin kai da gudummuwar dabaru tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro, ko Allah zai sa hakan ya kawo ƙarshen ta'addanci.

Tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu da gwamna El-Rufai.
Ina goyon bayan El-Rufa'i, ya kamata mu tura yan ta'adda Lahira, Tinubu Hoto: Kaduna Political Affairs/facebook
Asali: Facebook

Da yake jawabi, Tinubu ya ce ya yarda da kalaman El-Rufa'i na cewa duk wani abu da ake bukata na kashe yan ta'adda ya kamata a gaggauta yin shi.

Bola Tinubu ya ce:

"Ni ba kwararre bane a fannin tsaro, amma ina tare da shi (El-Rufa'i), a saukake ina bayansa kan duk abin da zamu yi na kawo karshen matsalar tsaro da kuma sheƙe makiyan cigaba a kowane lokaci."

Ɗan takarar shugaban ƙasan ya ce duk abinda ya shafi rayuwar ɗan Najeriya ɗaya, ya shafi kowa, ya jaddada bukatar matsawa a yaƙi da jajircewa, amfani da wasu dabaru kamar na fasaha wajen kawo karshen lamarin.

Kara karanta wannan

Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m

Mu taimaka wa waɗan da harin ya shafa - Tinubu

Tinubu ya roki yan Najeriya su ba da gudummuwa dai-dai gwargwagdo a kokarin da ake na rage wa waɗan da wannan abu ya shafa raɗaɗi.

"Na zo nan ne jajantawa gwamna El-Rufai da al'ummar Kaduna kan harin jirgin ƙasa. Bala'i ne da ya shafi ƙasa baki ɗaya, abun ya taɓa kowa da kowa."
"Zubda jini ya yawaita a Najeriya, muna bukatar yaƙar ta'addanci da duk abin da muka mallaka. An kashe wasu mutane wasu kuma an neme su an rasa. Abun da takaici."

Bayan haka ne, Tinubu ya bayyana wa gwamnan Kadunan cewa ya ba da tallafin miliyan N50m domin tallafawa mutanen da harin ya shafa.

A wani labarin kuma Matar Aure mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure

Wata mata saboda tsabar kishi ta ɗaɓa wa Maigidanta wuƙa har lahira saboda ya shaida mata zai ƙara Aure daga kauyen su.

Kara karanta wannan

Ramadan: Bola Tinubu ya yi kira na musamman ga al’ummar Musulmi a kan watan azumi

Lamarin ya auku a jihar Oyo, kuma rahoto ya nuna cewa Matar yar shekara 43 ta halaka Mijin ne yana tsaka da bacci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel