Sheikh Nuru Khalid: Gaskiya 6 game da limamin da aka kora saboda sukar gwamnatin Buhari

Sheikh Nuru Khalid: Gaskiya 6 game da limamin da aka kora saboda sukar gwamnatin Buhari

Ya zuwa ranar Asabar 2 ga watan Afrilu, Sheikh Muhammad Nuru Khalid shi ne babban limamin masallacin Juma'a na Apo da ke Abuja.

Kwamitin masallacin ya dakatar da shi ne a ranar Asabar din da ta gabata saboda hudubar da ya yi a ranar Juma’a, 1 ga Afrilu, inda ya caccaki gwamnatin Buhari kan gazawarta wajen shawo kan matsalar rashin tsaro da kashe-kashe a kasar.

Sheikh Nuru Khalid: Gaskiya 6 da ya kamata ku sani game da limamin da aka kora saboda sukar gwamnatin Buhari
Sheikh Nuru Khalid: Gaskiya 6 game da limamin da aka kora saboda sukar gwamnatin Buhari | Hoto: newsdigest.ng
Asali: UGC

A ranar Litinin 4 ga watan Afrilu ne shugaban kwamitin masallacin ya sanar da korar Sheikh Khalid gaba daya, inda ya ce malamin bai nuna nadamar matakin da aka dauka na dakatar dashi ba.

Wanene Sheikh Muhammad Nuru Khalid?

  1. Sheikh Khalid dan assalin jihar Filato ne
  2. An haifi fitaccen malamin addinin musuluncin ne a ranar 1 ga Oktoba, 1960, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC Pidgin ta ruwaito
  3. Sheikh Khalid ya yi karatunsa na Boko da na Islama a garin Jos, babban birnin jihar ta Filato
  4. Ya zama Babban Limamin Masallacin rukunin gidajen 'yan Majalisun Tarayya shiyyar E da ke, Gudu, Abuja, a 2007
  5. Kafin zamansa Babban Limamin Apo, Sheikh Khalid ya taba zama babban limamin masallacin Nyanya da ke Abuja
  6. Ana kuma kiransa da 'Digital Imam'
  7. Sheikh Khalid ya shahara a cikin shekaru biyu da suka gabata saboda jajircewarsa da sukar da yake yi wa hukumomin kasar nan

Kara karanta wannan

A Ƙarshe, Gwamnatin Buhari Ta Saki Hotunan Da Sunayen Waɗanda Ke Sace Wa Najeriya Ɗanyen Man Fetur

Cikakkiyar hudubar Juma’ar da ta jawo aka dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci a Apo

Legit.ng Hausa ta saurari wannan huduba ta Sheikh Nuru Khalid, ta fassara ta zuwa harshen Hausa. The Cable ta kawo asalin hudubar cikin harshen Ingilishi.

“Shin babu wanda zai dauki laifi ne? Ina ganin cewa dukkaninmu mun gaza. Ma’ana – Na gaza a matsayin Limami, na gagara fahimtar da ku cewa rai na da daraja.”
“Dukkanku kun gaza a matsayinku na iyaye wajen nunawa ‘ya ‘yanku cewa kashe-kashe ba abu mai kyau ba ne. Shugabanni, ‘yan siyasa, da gwamnoni sun gaza.”
“Musamman kuma mai girma shugaban kasar tarayyar Najeriya, ya ba mu kunya.”
"Mu na da bidiyonka ka na fadawa ‘Yan Najeriya cewa sojojinmu ba su gaza ba, su na duk abin da ake bukata na shawo kan matsalar tsaro da zarar ka samu mulki.”

Kara karanta wannan

Hadimar Buhari ta sanar da hakikanin dalilin korar Sheikh Nuru Khalid daga limanci

“An ba ka shekaru hudu, har da kari amma ana kashe mutane kamar tsuntsaye. Kisan rai ya na nema ya zama abin da aka saba da shi a karkashin mulkinka (Buhari).”

Babu hankali a lamarin: Martanin Shehu Sani da wasu 'yan Najeriya kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid

A wani labarin, an caccaki kwamitin masallacin Abuja bayan dakatar da limamin masallacin Juma'a na Apo Sheikh Nuru Khalid sakamakon caccakar bangarori daban-daban na gwamnati.

Daya daga cikin wadanda suka yi Allah-wadai da matakin dakatar da malamin dai shi ne tsohon dan majalisar dattawa daga Kaduna ta tsakiya kuma mai fafutukar siyasa da zamantakewa, Shehu Sani.

Sani ya bi sahun ‘yan Najeriya da dama don bayyana ra’ayinsa a shafin Twitter. Ya bayyana dakatarwar a matsayin rashin hankali tsagwaronsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel