A Ƙarshe, Gwamnatin Buhari Ta Saki Sunaye Da Hotunan Waɗanda Ke Sace Wa Najeriya Ɗanyen Man Fetur

A Ƙarshe, Gwamnatin Buhari Ta Saki Sunaye Da Hotunan Waɗanda Ke Sace Wa Najeriya Ɗanyen Man Fetur

  • Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta yi kasa a gwiwa ba wurin daukan mataki kan masu satar danyen mai
  • A yayin wani zaman shari'a a kotun tarayya da ke Jihar Rivers, an yanke wa mutum biyar hukuncin dauri saboda safarar danyen mai ba bisa ka'ida ba
  • Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ce ta gurfanar da mutanen biyar, ta wallafa sunayensu da hotunansu a intanet

Port Harcourt, Rivers - Kotun Gwamnatin Tarayya a Port Harcourt, babban birnin Jihar Rivers ta yanke hukuncin daurin gidan yari ga wasu mutane biyar saboda satar danyen man fetur.

Kamar yadda hadimar Shugaba Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta wallafa a Twitter, an gurfanar da wadanda aka yanke wa hukuncin ne bisa dillancin danyen man fetur ba tare da lasisi ba.

Kara karanta wannan

Sheikh Nuru Khalid: Gaskiya 6 game da limamin da aka kora saboda sukar gwamnatin Buhari

A Ƙarshe, Gwamnatin Buhari Ta Saki Sunaye Da Hotunan Waɗanda Ke Sace Wa Najeriya Ɗanyen Man Fetur
Wasu mutane biyar da aka yanke wa hukunci saboda satar danyen man fetur. Hoto: EFCC
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin sakon da hadimar shugaban kasar ta wallafa, ya nuna cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'anatti, EFCC, ce ta gurfanar da su a gaban kotun.

Wadanda ake zargin sune:

  1. Wei Ibolo
  2. Mudashiru Toaheed
  3. Etim Edet
  4. Martins Savior
  5. Tope Alani

Kwastam Ta Kama Motar Dangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

A bangare guda, Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami'an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.

Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hadimar Buhari ta sanar da hakikanin dalilin korar Sheikh Nuru Khalid daga limanci

Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164