Yanzu-Yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da ke neman tsige gwamnan APC
- Kotun daukaka kara ta yi watsi da bukatar da aka shigar domin neman tsige gwamnan jihar Ebonyi David Umahi
- Wannan na zuwa bayan da wasu 'yan siyasar jihar a jam'iyyar APC suka nemi a tsige shi da mataimakinsa
- Wannan rikici dai ya faro ne tun bayan da Umahi da mataimakinsa suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga PDP
Enugu - Kotun daukaka kara reshen Enugu, a ranar Juma’a ta kori karar da ke neman a tsige Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi da mataimakinsa Kelechi Igwe daga ofis saboda sauya sheka zuwa wata jam’iyya.
'Yan siyasan biyu sun koma jam'iyyar APC ne daga jam’iyyar PDP a watan Nuwamban 2020, Premium Times ta ruwaito.
Bayan sauya shekar tasu, dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamna na 2019, Sonni Ogbuoji, da mataimakinsa, Justin Mbam, sun garzaya wata babbar kotun jihar Ebonyi suna neman ta kori gwamnan da mataimakinsa daga kujerunsu.
Masu shigar da karar sun bukaci kotun da ta tsige gwamnan da mataimakinsa daga kujerunsu gwamna a matsayin wanda ba kowa ba ne saboda sauya shekarsu daga PDP zuwa APC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Messrs Ogbuoji da Mbam sun kuma bukaci kotun da ta bayar da umarnin a rantsar da su cikin gaggawa tunda sun zo na biyu a zaben gwamna na 2019, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Amma babbar kotun da ta yanke hukunci a ranar 28 ga watan Fabrairu ta kori karar tare da bayar da N500,000 a matsayin diyya ga wadanda suka shigar da karar.
Kasancewar ba su gamsu da hukuncin ba, masu shigar da karar sun daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yanke.
A hukuncin da ta yanke, a ranar Juma’a, kotun daukaka kara ta amince da hukuncin da karamar kotun ta yanke kan lamarin.
Alkalin kotun daukaka kara, a hukuncinta ta yi watsi da karar saboda sabawa kundin tsarin mulki da dokokin Najeriya.
Tsige Umahi: INEC ta ce ba za ta baiwa PDP kejurun Gwamna da 'yan majalisun 16 ba, ta bada dalilli
A wani labarin, hukumar zabe mai zaman kanta INEC, a ranar Alhamis ta ce ba za ta dauki wani mataki ba game da hukuncin kotu na tsige Dave Umahi a matsayin gwamnan Ebonyi bisa sauya sheka daga PDP zuwa APC a 2020.
Hukumar ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban sashin watsa labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, rahoton The Punch.
A cewar hukumar zaben, ta samu hukunce-hukuncen kotu har guda 12 dangane da batun sauya shekar Umahi; mataimakinsa Kelechi Igwe, da yan majalisar jiha guda 16.
Asali: Legit.ng