Tirkashi: Jami'an Kwastam Sun Kama 'Ɗan Sanda' Da Mota Maƙare Da Haramtacciyar Shinkafa a Katsina
Jihar Katsina - Hukumar Kwastam, NCS, reshen Jihar Katsina ta kama buhunan aya, shinkafar kasar waje da motocci da wasu kayayyakin da kudinsu ya kai N42.793m, Daily Trust ta rahoto.
Rundunar ta kuma ce ta kama wani da ake zargi, da ya yi ikirarin cewa shi dan sanda ne da buhunan shinkafa 25 da aka shigo da su ta haramtacciyar hanya.
Mukadashin kwantrola, DC Dalha Wada Chedi, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, ranar Laraba a Katsina, yana cewa an yi kwacen ne daga 1 ga watan Fabrairu zuwa yanzu.
Haramtattun kayayakin da kwastam suka kama da kudinsu
Chedi ya ce rundunar ta kwace buhunan aya 400, da kudinsa ya kai Naira miliyan 10 cikin wata babban mota DAF, da ya kamata a biya musu kudin haraji na N6.750m.
"A cikin lokacin, mun yi nasarar kwace buhunan shinkafan kasar waje 432 da kudinsu ya kai N10.454m da motocci da kudinsa ya dara N10.9m.
"Kazalika, jami'an mu sunyi nasarar kwace katon din taliya sifageti katon 309, makaroni ta kasar waje katon 55, jarkokin man gyada 68 da jarkokin man fetur 284," in ji shi.
Kwantrolan ya kara da cewa sun kwace katon din madaran kasashen waje 69, madara mai kauri da kasar waje katon 30, kunshin kayan gwanjo 15.
Sauran kayan sun hada da kulin tufafi gwanjo 40 da katon din magani shida.
An kama dan sandan dauke da haramtattun shinkafa da katin shaida hudu
Ya ce:
"Yana da muhimmanci a bayyana cewa a ranar 23 ga watan Maris, mun kama wata tsohuwar Toyota Sienna dauke buhun shinkafar kasar waje 25, da katon din sifageti da kasar waje da makaroni.
"An kama motar ne mai dauke da rubutu '‘Federal Joint Compliance, Monitoring and Enforcement against Multiple Taxes and Levies' a babban titin Katsina zuwa Kaduna.
"Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa shi dan sanda ne, an kuma same shi da katin shaidar aiki daban-daban har gudu hudu da wasu kayayakin."
Chedi ya ce an mika fiye da katon din magunguna 253 da aka kama ga Hukumar NAFDAC.
Asali: Legit.ng