Da duminsa: 'Yan bindiga sun halaka jama'a masu yawa a sabon harin da suka kai Benue
- Sabon farmakin 'yan ta'adda a garun Naka da ke karamar hukumar Gwer ta jihar Benue ya yi ajalin jama'a masu yawa
- An gano cewa miyagun sun bayyana da yawansu a kan babura inda suka fara harbe-harbe yayin da jama'a suka dinga gudun tsira
- Shugabar karamar hukumar Gwer, Grace Igbabon, ta tabbatar da aukuwar lamarin inda tace a take maharan suka halaka mutum 3
Benue - An kashe mutane uku a wani farmakin da aka kai garin Naka da ke karamar hukumar Gwer ta yamma a jihar Benue.
Harin ya faru sa’o’i 24 bayan kashe wani Faston cocin Deeper Life da wasu mutane uku a karamar hukumar Guma da ke jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Naka, wani gari kasuwanci na karkara kuma hedkwatar karamar hukumar Gwer ta Yamma, ya zama mai masaukin baki ga ‘yan gudun hijira daga kauyukan yankin.
Majiyoyi sun ce sabon harin da aka kai a garin ya faru da misalin karfe 8 na daren ranar Talata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani mazaunin garin ya ce mutane sun fara gudu ta biyo bayan karar harbe-harbe da aka yi a kusa da Kwalejin Comprehensive da ke Naka.
Mazauna garin sun yi zargin cewa maharan da ke sanye da kakin sojoji sun kashe mutane uku a nan take kafin a fatattake su.
Shugabar Gwer West, Grace Igbabon, ta shaida wa manema labarai cewa maharan sun bayyana a kan babura.
“Wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a wata unguwa da ke bayan garin Naka, sun zo da yammacin ranar Talata. Sun bayyana da kakin sojoji kuma suna kan babura."
“Harin da aka kai a Naka da ke kusa da babban birnin jihar ya yi fallasa cewa babu zaman lafiya a Makurdi domin a wani lokaci sun mamaye garin Adaka da ke wajen babban birnin jihar.
“Mutane uku ne aka kashe a cikin lamarin sun hada da, tsofaffi biyu da saurayi daya. An yi ta harbe-harbe sosai kuma mutane suna gudu ne domin ceton ransu.
“Na kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda da kuma mai baiwa Gwamna shawara kan harkokin tsaro, na kuma aika masa da hotunan wadanda suka mutu,” in ji Igbabon.
Da aka tuntubi shugaban kungiyar Myetti Allah Cattle Breeders Association (MACBAN) na jihar, Mohammed Risku, ya ce bai san da faruwar lamarin ba, yana mai jaddada cewa har ya kammala ganawa da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro.
A halin da ake ciki, basaraken gargajiya na karamar hukumar Ter Nagi, Cif Daniel Abomtse, ya shaida wa manema labarai a Makurdi cewa maharan sun kashe mutanensa uku.
Wata sabuwa: Ƴan sanda sun daƙile harin da miyagu suka kai matatar man fetur ta Ɗangote
A wani labari na daban, Jami'an tsaro sun bankaɗo yunƙurin kai farmaki matatar man fetur ta Dangote, dake Lekki Free Trade Zone cikin jihar Legas.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fita ranar Talata.
Kamar yadda kakakin ya bayyana, harin ya auku ne a safiyar Litinin, Vanguard ta ruwaito. Ya ce, an daƙile harin da hatsabiban suka yi yunkurin kaiwa ne, yayin kokarin awon gaba da keburan karfen da aka riga aka saka cikin matatar.
Asali: Legit.ng