Buhari ya nemi Sanatoci su tabbatar da sababbin mukamai 5 da ya nada a hukumomin gwamnati

Buhari ya nemi Sanatoci su tabbatar da sababbin mukamai 5 da ya nada a hukumomin gwamnati

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya aika takarda zuwa majalisar dattawa a kan nadin wasu mukamai
  • Mai girma shugaban Najeriyan ya nemi a tabbatar masa da wasu kwamishinoni 4 a hukumar NURC
  • A wata wasikar, Buhari ya bukaci a amince da nadin babban kwamishina na REC a hukumar INEC

Abuja - A ranar 29 ga watan Maris 2022, majalisar dattawa ta karbi wata wasika da ta fito daga ofishin Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

This Day ta ce takardar shugaban Najeriyar ta nemi amincewar Sanatoci wajen tabbatar da nadin mutum hudu a matsayin kwamishinonin hukumar NURC.

Legit.ng ta ce tun a ranar Alhamis da ta wuce shugaba Muhammadu Buhari ya aiko da wannan bukata, da sai a jiya aka iya karanto ta a zauren majalisar.

Shugaban majalisar dattawa na kasa, Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ne ya gabatar da rokon shugaban kasar domin a tabbatar da wadannan nadin mukamai a jiya.

Kara karanta wannan

Tinubu @ 70: Buhari ya tura masa sakon taya murna, ya fadi halayen Tinubu na kirki

Daya daga cikin hadiman shugaban majalisar, Ezrel Tabiowo ya tabbatar da haka a wani jawabi.

"Kamar yadda sashe na 11(3) na dokar PIA ta shekarar 2021 tayi tanadi, ina mai gabatarwa majalisar dattawan nadin kwamishinoni a hukumar NURC."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Muhammadu Buhari

Sanatoci
'Yan Majalisar Dattawa Hoto: Tope Brown / @NgrSenate
Asali: Facebook

Su wanene za su hau kujerun NURC

Kamar yadda labari ya zo mana, wadanda aka zaba su ne: Dr. Nuhu Habib (Arewa maso yamma, jihar Kano) da zai zama babban kwamishinan samar da mai.

Akwai Dr. Kelechi Onyekachi Ofoegbu (Kudu maso gabas, jihar Imo) a matsayin babban kwamishinan muhimman tsare-tsare da kula da tattalin arziki.

Sauran sun hada da Kyaftin Tonlagha Roland John (Kudu maso kudu, jihar Delta) wanda zai rike kujerar kwamishinan kula da lafiya, da muhalli da al’umma.

Na karshe a jerin shi ne Jide Adeola (Arewa maso Arewa, jihar Kogi), wanda ake so ‘yan majalisa su tabbatar da shi a matsayin sabon kwamishinan gudanarwa.

Kara karanta wannan

Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da Abdullahi Adamu, mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC

An samu sabon REC a INEC

A wata wasikar ta dabam kuma, an bukaci a tantance Dr. Hale Gabriel Longpet a matsayin kwamishinan yanki na hukumar INEC mai wakiltar jihar Filato.

Hukumar Nigerian Upstream Regulatory Commission watau NURC ta na cikin masu kula da harkar mai.

Inda Buhari ya samu cikas - Lai

A makon nan ne aka samu rahoto mai cewa Ministan yada labarai da al’adun kasa, Lai Mohammed ya kare gwamnatin Muhammadu Buhari daga sukar jama'a.

Lai Mohammed ya ce har yanzu ana ta kokarin gyara barnar da 'Yan PDP suka yi a baya ne. Ministan ya ce shekaru hudu sun yi kadan a shawo kan matsalolin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel