Harin jirgin kasa: An gano gawarwakin mutane da yawa a wurin da 'yan bindiga suka kai hari, Gwamnatin Kaduna
- Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da cewar an rasa rayuka a harin da yan bindiga suka kai kan jirgin kasa a jihar
- Gwamnatin Kadunan ta ce tuni hukumomin agaji suka kwashe gawarwakin zuwa asibitocin jihar
- Sai dai ba a bayyana ainahin yawan mutanen da suka kwanta dama ba a harin na ranar Litinin
Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da cewar an rasa rayuka a harin ta’addanci da aka kai kan jirgin kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Talata dauke da sa hannun kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, Daily Trust ta rahoto.
Sai dai kuma, Aruwan bai bayyana adadin mutanen da suka mutu ba amma ya ce an kwashi wadanda suka rasa rayukan nasu da wadanda suka jikkata zuwa asibiti. Ba a kuma ambaci sunan asibitin da aka kaisu ba.
Aruwan ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“A safiyar yau ne jami’an tsaro da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna (SEMA) da kungiyar agaji ta Red Cross suka kammala kwashe fasinjojin da ke cikin jirgin kasa mai zuwa Kaduna daga Abuja.
“An kwashi fasinjojin da suka jikkata da sauran da suka mutu zuwa asibitoci. An kwashi fasinjojin ne daga wurare daba-daban masu wuyar zuwa a jeji da wurare masu tsauni da ke Audujongom, hanyar Kaduna zuwa Abuja.
“Kamar yadda aka bayyana a jiya, Gwamnatin Jihar Kaduna tana ci gaba da tuntubar Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) don tabbatar da jerin fasinjojin da ke ciki domin gano inda suke da kyau.”
Aruwan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya yaba ma wadanda suka yi aiki kwasar fasinjojin sannan ya roki asibitocin da su kula da wadanda abun ya ritsa da su da kyau.
Ya ce gwamnan ya kuma umurci ma’aikatar lafiya da ta tuntubi asibitocin, inda ya bayyana cewa gwamnati za ta dauki nauyin maganinsu.
Ya kara da cewa:
"A daidai lokacin kawo wannan rahoton, ana ci gaba da ayyukan bincike da ceto."
A rahoton Tribune, shugabar NRC Fidet Okhiria, ta yi bayanin cewa mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a harin na daren Litinin.
Yan bindiga sun tada Bam kan jirgin kasan Abuja-Kaduna mai dauke da fasinjoji 900
A baya mun ji cewa wasu tsagerun yan bindiga da ake zargin yan ta'adda ne sun tada Bam kan layin dogon jirgin kasan Abuja-Kaduna dauke da daruruwan fasinjoji.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa wannan hari ya auku ne da daren Litnin, tsakanin garin Katari da Rijana.
Daya daga cikin fasinjojin ya bayyana cewa yan bindigan sun zagaye jirgin kuma suka fara bude wuta.
Asali: Legit.ng