Bayan kashe mutum 50, 'Yan bin sun sake sheƙe dandazon mutane a jihar Kaduna

Bayan kashe mutum 50, 'Yan bin sun sake sheƙe dandazon mutane a jihar Kaduna

  • Yankin karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna sun tsinci kansu cikin mummunan tashin hankali
  • Bayan halaka kusan rayuka 50 a ƙauyuka 9, yan bindiga sun ƙara kashe wasu mutum 15 jiya Lahadi da daddare
  • Mazauna yankin sun tabbatar da cewa tun ranar Alhamis da ta gabata yan bindiga ke kawo hari suna kashe mutane

Kaduna - Aƙalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu yan bindiga suka farmaki ƙauyen Hayin Kanwa a gundumar Yakawada, ƙaramar hukumar Giwa, jihar Kaduna.

Lamarin ya faru kwana uku bayan halaka rayuka kusan 50 a yankin ƙauyuka 9 dake karamar hukumar Giwa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Wani mamban ƙungiyar Bijilanti ta Kaduna (KADVS), wanda ya nemi a ɓoye bayanansa ya shaida wa manema labarai cewa an sallaci Mamatan da safiyar yau Litinin.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa kowace rana ake ƙara samun zaman lafiya a Najeriya, Gwamnatin Buhari ta magantu

Yan bindiga sun.ƙara kashe mutane a Kaduna.
Bayan kashe mutum 50, 'Yan bin sun sake sheƙe dandazon mutane a jihar Kaduna Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ce lamarin tsaro a karamar hukumar Giwa ya ƙara taɓarɓarewa ya yi muni saboda kullum sai an kashe mutane tun daga ranar Alhamis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin ya ce:

"Yanayin ya ƙara muni saboda yan bindiga sun sake halaka mutum 15 a ƙauyen Hayin Kanwa jiya jiyan nan (Lahadi) da daddare. Tun ranar Alhamis, yan bindiga suke matsa wa kauyuka da kai hari suna kashe mutane."

Wani mazaunkn Giwa, wanda ya faɗi sunansa da Ridwan, ya gaya wa jaridar cewa yan bindiga suna kai hari ƙauyuka akai-akai.

Ridwan ya ce:

"Sun shigo ƙauyen kuma suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi wanda ya yi sanadin mutuwar waɗan nan mutanen. Shin kun san cewa ba mu samu damar ɗakko gawarwakin ba sai yau da safe?"

Ya kuma ƙara da cewa a halin yanzun yan bindiga sun fi kashe mutane a kan garkuwa da su domin neman kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Tsagin hamayya na kulla-kullan ruguza Najeriya' Gwamnatin Buhari ta fallasa sirrin

Hukumomi a Kaduna sun san da sabon harin?

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, bai ɗaga kiran wayar da aka masa kuma bai turo amsar sakon da aka tura masa ba game da lamarin.

Haka zalika kiran wayar da aka yi wa kakakin rundunar yan sanda na jihar, ASP Jalige Mohammed, bai amsa ko ɗaya ba domin jin ta bakinsa.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari Kaduna, sun tattara maza da mata 47

Yan ta'adda sun kai hari ƙauyen Agunu Dutse dake ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna da tsakar daren Alhamis.

Bayanai daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun jikkata wani da harbi, sun kuma yi awon gaba da mutum 47.

Asali: Legit.ng

Online view pixel