Da dumi-dumi: Yan sanda sun karbe majalisar Cross River bayan tsige yan majalisa 20
- An tsaurara matakan tsaro a harabar majalisar dokokin jihar Cross River
- Hakan ya biyo bayan tsige yan majalisa 20 da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi a ranar Litinin kan sauya sheka daga PDP zuwa APC
- Jami'an yan sanda na sashi daban-daban ne suka karbe majalisar tun daga karfe 6:00 na asuba
Cross River - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sashi daban-daban na rundunar yan sandan Najeriya sun karbe dukka hanyoyin da ke sada mutum ga harabar majalisar dokokin jihar Cross River.
Sun mamaye wuraren ne tun da misalin karfe 6:00 na asubahi kamar yadda shaidu suka bayyana.
Sashin yan sandan da ke kasa sun hada da na yaki da garkuwa da mutane, masu yaki da kungiyar asiri da kuma jami’an yan sanda na yau da kullum, dukkansu dauke da makamai.
The Sun ta kuma rahoto cewa an hangi wasun su na cikin harabar majalisar dokokin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kuma gano wasu daga cikin jami’an yan sandan tsaye kusa da ofishin Gwamna Ben Ayade wanda bai da nisa da wajen.
A daya bangaren majalisar akwai filin wasa na UJ Esuene Stadium Calabar. An kuma gano wasu mutane da ake zaton magoya bayan jam’iyyar siyasa ne suna zukar hayaki da shan lemuka masu zafi.
Masu ababen hawa da masu wucewa na fuskantar matsala wajen kutsawa cikin cunkoson jami’an tsaro da motocinsu.
An tattaro cewa an tsaurara matakan tsaron ne biyo bayan hukuncin da mai shari’a Taiwo Taiwo ya yanke a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ta kori ‘yan majalisar jihar 18 da kuma wasu ‘yan majalisar wakilai guda biyu kan sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress.
Jam’iyyar APC mai mulki ta yi ikirarin cewa ta shigar da kara kotu domin a dakatar da aiwatar da hukuncin, yayin da jam’iyyar ta garzaya zuwa kotun daukaka kara.
Kotu ta kwace kujerun wasu yan majalisa 20 saboda komawa APC
A baya mun kawo cewa babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta sallami wasu mambobin majalisar dokokin jihar Cross River su 20 a ranar Litinin, 21 ga watan Maris.
Kotu ta kwace kujerun su ne saboda sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki.
Kotun, a wani hukunci da mai shari’a Taiwo Taiwo ya yanke, ya riki cewa ya zama dole yan majalisar su sauka daga kujerunsu kasancewar sun yi watsi da jam’iyyar da ta dauki nauyin kawo su kan mulki.
Asali: Legit.ng